Jin zafi a lokacin jima’i shi ake kira “dyspareunia” a likitance.


TAMBAYA DAGA MEMBER

Aslm. Ina Mika godiya ta wa Malaman gidan Nan bisa gudummawa da suke badawa Allah ya saka musu da mafificin alkhairi, Dan Allah admin Ina roko da a boye sunana, Miyake kawo lkcn da Muka kasance da mijina idan zai shigeni Ina Jin zafi sosai sannan bayan mun gama sai side daya ya kunbura kuma yana min ciwo sosai, kuma bayan mun gama sai na kalla harda jini2 ya gauraya, naje asibiti an rubutamin magani da allura Amma baidaina ba 3mnth da aure Dan Allah ataimaka Min ayi hakuri da dogon rubutu na. Kayi hakuri Dr da biyoka private danayi na tura group Bai tafiba Amin afuwa pls.

AMSA

Jin zafi a lokacin jima’i shi ake kira “dyspareunia” a likitance. jin zafin zai iya samun mata ko maza, matasa ko masu nisan shekaru. Bayan haka, jin zafin zai iya kasancewa a daidai lokacin da ake yin jima’in ne ko kuma bayan an gama yin jima’in. 

Ga mata, zai iya zamowa daga farkon farji ne (externally) wanda ya kunshi labba guda biyu da suke rufe mashigar farji (labia majora and labia minora), ko dan-tsaka (clitoris), ko farkon ramin farji (vaginal canal). Zafin zai iya zamowa kuma daga can cikin farjin ne (internally), wanda ya kunshi mabiyiya (cervix), ko mahaifa (uterus), ko mara (pelvis). Ga maza, jin zafin zai iya zamowa a kan azzakari ne (glans penis), ko bututun azzakari (corpus cavernosa), ko mara (pelvis).

Jin zafin ga mace a lokacin da mijinta zai shigeta (intraorbital or superficial dyspareunia), yakan faru ne saboda rashin ni’ima (lack of lubrication) wanda rashin yin gamsasshen wasannin motsa sha’awa yakan haifar, ko rauni (injury), ko kamuwa da kwayoyin cuta (infection) a farji. Sa’annan jin zafin da takeyi bayan da mijinta ya shigeta sosai (collision dyspareunia) yakan faru ne sakamakon cututtuka kamar kumburin mahaifa (endometriosis), cututtukan sanyin mara (pelvic inflammatory diseases – PIDs), zazzagowar mahaifa (uterine prolapse), karkacewar bakin mahaifa (retroverted uterus), karin mahaifa (uterine fibroids), taruwar ruwa a cikin mahaifa (cystitis), kumburin hanji (irritable bowel syndrome), matsalolin bangon mara (pelvic floor dysfunction), tsiron tsoka a cikin mahaifa (adenomyosis), cutar basir (hemorrhoids), kurajen mahaifa (ovarian cysts), da tiyata (surgery) wacce ta shafi mara ko mahaifa.

Amma ya kamata mu fahimci cewa tsananin tsawo ko girman azzakarin namiji bai zai zamo dalilin jin zafin saduwar aure ba, sai idan hakan ya hadu da rashin ni’ima sakamakon rashin gamsasshen wasannin motsa sha’awa. Dalilin haka shine Allah SwT ya halicci farjin mace da yanayin budewa (elasticity) a lokacin saduwar aure domin ya iya daukar al’aurar namiji komai girmanta. Zamu iya yarda da hakan ta ganin yadda jariri yake iya fitowa ta cikinsa. Nasan kuwa mawuyaci ne a sani al’aurar namijin da takai girman jariri.

Sa’annan jin zafin saduwa ya rabu gida hudu kamar haka:

1. Wanda mace take jinsa tun lokacin da tayi aure aka fara saduwa da ita kuma bai daina daga baya ba (primary dyspareunia). Abubuwan da suke haddasa shi sune cututtukan al’aurar mace (female vaginal infections), cututtukan sanyin mara na mata (PIDs), Karin mahaifa (uterine fibroids), makalewar halittun mara a jikin juna (pelvic adhesion), rashin daidaiton sinadarai (hormonal imbalance), rashin kwanciyar hankali a rayuwar aure (marital psychological factors).

2. Wanda mace ta fara jinsa daga baya alhalin dacan ba haka take ba (secondary dyspareunia). Abubuwanda suke haifar dashi iri daya ne da na primary dyspareunia. Abunda yake kari akai shine gabatowar daukewar al’ada (menopause).

3. Wanda mace take jinsa a duk lokacinda mijinta yake saduwa da ita (complete dyspareunia). Shima duk abubuwanda suke haifar da primary da secondary dyspareunia sune suke kawo shi.

4. Wanda mace take jinsa lokaci-lokaci (situational dyspareunia). Shine wanda mace take jinsa a wasu kebantattun lokuta, kamar salon saduwa (sex style), 

Shi kuma jin zafin saduwa ga namiji yana faruwa ne saboda dalilai kamar haka:

1. Dadewar fatar kan mazakuta (foreskin damage) wanda yake faruwa saboda rashin damshi a lokacin saduwa, ko kuraje a wurin.

2. Kamuwa da cututtukan da ake dauka a lokacin jima’i (sexulallytransmitted infections - STIs) kamar herpes ko gonorrhea.

3. Nakasa a halittar mazakuta (penile deformity) kamar karkacewar mazakuta (peyronie’s disease).

4. Rashin kwanciyar mazakuta bayan gama saduwar aure (priapism) wanda yakan faru saboda kin fitar jiki daga mazakuta bayan an gama saduwar. Don haka mazakutar zata kasance a mike lokaci mai tsawo, sai mutum ya rika jin zafi.

Idan jin zafi lokacin saduwa ya hadu da fitar jini, to, a binciki yiwuwar kamuwa da wasu cututtuka wanda ta hanyar awon asibiti ne kadai za’a iya tabbatarwa. Sa’annan ana iya magance jin zafin saduwa ne ta hayar magance dalilin da ya haddasa shi. Saboda haka idan amarya tana jin zafin saduwar aure, to, a binciki abubuwanda na fada. Saidai mafi yawan lokaci da zarar an samar da isasshiyar ni’ima, za’a magance matsalar.

Post a Comment

0 Comments