ME KESA DA ZARAN MUTUM YAYI INZALI SAI AZZAKARIN SA YA KWANTA SAI BAYAN 30 MINUTES KO 1 HOUR SANNAN YA KARA MIKEWA ?


ME KESA DA ZARAN MUTUM YAYI INZALI SAI AZZAKARIN SA YA KWANTA SAI BAYAN 30 MINUTES KO 1 HOUR SANNAN YA KARA MIKEWA ? 

amsa : usman shehu hassan. 

SHARE 🌾🌿💕 

Yin inzali shine kololuwar gamsuwar namiji idan yana saduwar aure da matarsa. Da zarar yakai wannan matsayin, to, sha’awarsa zata kwanta nan take, kuma a mafi yawan lokuta ba zai iya tayarda sha’awar ba sai bayan wani lokaci mai dan tsawo. Wannan lokacin hutawar shine ake kira “refractory period” a likitance, watau lokacin daukewar sha’awa. Ayyukan jiki (physiological factors) da kuma ayyukan kwakwalwa (psychological factors) sune suke da matukar tasiri akan tsowon lokacin da mutum zai dauka na daukewar sha’awa, kafin ya sake murmurewa, watau ya komawa ruwa.

Bayanin yadda al’amarin yake faruwa shine kamar haka:

Amsawar kwakwalwa da kuma laka (neural response) idan mutum yakai kololuwar sha’awa: Motsawar sha’awar namiji a lokacin da zai sadu da iyalinsa ita ce take haifar da karuwar gudanar jini a cikin mazakutarsa. Daga nan sai mazakutar ta mike tsaye kyam. Idan kuwa zaiyi inzali (ejaculation), to, sai jijiyoyin kwakwalwarsa masu aikewa da jini a dukkan sassan jikinsa (parasympathetic nervous system) su amshi ragamar jin dadin saduwar da yakeyi. Hakan zai sanya ruwayen sinadai masu yawa wadanda suke kai sako zuwa kowane sako na jikinsa (neurotransmitters) suyi ambaliya a kowane sashi na jikinsa. A cikin sinadaran akwai “oxytocin” da “prolactin”.

Saboda jin dadin saduwar aure da oxyocin yake haifarwa shi yasa ake kiransa “cuddle hormone”, watau sinarin runguma. Sa’annan zubowarsa a lokacin yin inzali yana sanya matukar mutuwar jikin namiji. Shi kuwa sinadarin prolactin yana zubowa ne da zarar mutun yayi inzalin, ma’ana lokacin da hutun shawar ya fara. Amfaninsa a wannan lokacin shine ya kara tabbatar da gamsuwar da saduwar.

Shi kuma tsawon lokacin da namiji yake dauka kafin sha’warsa ta sake motsawa bayan yin inzali, shine ake kira “recovery time” a likitance. Ya bambanta a tsakanin mutane. Abubuwan da suke haddasa bambancin sune shekarun rayuwa (age), lafiyar jiki (health condition), sabo da yin jima’i (sexual experience), da yawan sinadarai a cikin jiki (body hormonal levels). Watau mafi yawan lokaci mutanen da suke cikin shekarun kuruciya, da wadanda basu da wata rashin lafiya mai tsanani, da mutanen da suke da yawan sinadari a jiki sakamakon jin abubuwa masu gina jiki, sunfi saurin murmurewa daga hutun daukewar sha’awa.

Sinadarin testosterone yana taka muhimmiyar rawa wajen motsa sha’war namiji, kuma abinci masu gina jiki sukan taimaka wajen samar dashi. Idan mutum yana bukatar saurin murmurewar, to, sai ya dage wajen cin kayan dadi, kuma masu gina jiki. Su kuma ayyukan motasa jiki suna taimakawa wajen samun ingantacciyar lafiya da kubuta daga manyan cututtuka. Idan mutum yana bukatar saurin murmurewar, to, sai ya dage wajen yin ayyukan motsa jiki. Zama cikin walwala da rashin bacin rai shima yana taimakawa kwarai. Sa’annan wani babban abu da yake kawo saurin murmurewa daga hutun sha’awar saduwa shine wasannin motsa sha’awa tsakanin ma’aurata kodai kafin fara saduwar ko kuma a lokacin da ake bukatar komawa.

Saidai ya kamata mu San cewa rashin saurin murmurewar ba wata cuta bace ko kuma gazawar kamar yadda bahaushe yake dauka. Wasu mutanen haka Allah yayisu, babu yadda za'a iya canzasu.

Allah ya bamu ikon saurin murmurewa, amin.

Post a Comment

0 Comments