RASHIN SANIN YANDA AKE SADUWAR AURE TSAKANIN MACCE DA NAMIJI NA DAGA CIKIN DALILAN DAYASA MATAN AURE KE NEMAN MAZA A WAJE SAMA DA TALAUCI..


RASHIN SANIN YANDA AKE SADUWAR AURE TSAKANIN MACCE DA NAMIJI NA DAGA CIKIN DALILAN DAYASA MATAN AURE KE NEMAN MAZA A WAJE SAMA DA TALAUCI..

A iya bincike na akan wannan matsalar sama da kaso 80% cikin Dari na maza basusan komai ba basu iya komai ba akan abunda ya shafi kwanciya da macce saidai abunda mata ke kira CI KA TASHI🙈🙈🙈. Wannan kuma yasamo asali ne daga tsananin kunyar da maza keji akan tattaunawa da junansu akan abunda ya shafi kwanciyar aure.

Kwanciyar aure kusan ince abu ne mai matukar muhimmanci kuma wajibi, saboda Shi din kanshi sashe ne a jikin dan adam mai zaman kansa wati (REPRODUCTIVE SYSTEM). yanda jiki ke bukatar ci da sha da fitsari da numfashi haka jiki ke bukatar saduwa. Kuma ko a addinance anyi magana mai yawa akan abunda ya shafi saduwa da kaucewa zinace zinace shiyasa Allah da manzon sa suka saukaka lamarin Aure.

ABUBUWAN DA YAKAMATA MU SANI

1️⃣. Maza basa tattaunawa akan abunda ya shafi kwanciyar aure saidai suyi magana ko taimakon juna akan maganin karfin maza da maganin basir. Zakuji mai maganin gargajiya ya dora speaker 🔊 a kasuwa yana sayarda magani yana cewa sai kayi rounds 5 na saduwa sannan kazama NAMIJI 😭😭😭 alhalin round daya wanda zaka gamsu matarka ta gamsu ya Wadatar a addinance a Likitance.

2️⃣. Gamsuwa ko jin dadin saduwa mataki mataki ne. Binciken masana ya nuna mata masu kananan shekaru wato kamar 18 zuwa 22 sunfi mata masu shekara 23 zuwa 40 saurin kawowa idan ana saduwa dasu, amma duk da haka akwai wadansu abubuwa da suke iya canja wanann hasashen kamar tsananin sha'awa da kuma tsananin so ko akasin hakan.
A lokacin da namiji yake saduwa da macce idan basu gabatar da kowadanne wassanni da romances ba, bincike ya tabbatar sai namijin ya riga maccen kawowa, saboda idan akayi amfani da SCALE OF 7 na saduwa wato daga sanda ka fara saduwar kana scale na 1 har sanda zakayi release shine scale na 7. A lokacin da namiji yakai 7 zaiyi wahala maccen da shekarun ta sukakai 25 zuwa 35 kugan takai scale lamba 4, wata ma a 3 kawai take tsayawa... Mata dayawa suna korafi wa mata yan uwansu basu samun kawowa mazajen su ke sauka akan su.. Wannan yana daga cikin dalilan dake sa mata BIN MAZAN WAJE ko FADAWA HARKAN LESBIANISM da sauran su dan gusar da sha'awar su. 😭😭😭

3️⃣. Binciken wasu PSYCHOSOCIOLOGIST ya nuna, mata suna iya jure talaucin namiji idan zaibar macce ta nema ma kanta kudin lalura komai talaucin sa zata zauna dashi idan yana gamsar da ita a SADUWAR AURE, amma bazata jure arziki da rashin gamsar da ita a SADUWAR AURE ba dole sai ta bi mazan waje ko ta fada harkan LESBIANISM. tohhhh kunga anan yakamata malaman Addini suyi amfani da wannan hanyar dan toshe kofar zinace zinace da matan Aure keyi a yanzu.

4️⃣. Yakamata kai namiji ka fahimce jikin matarka, ma'ana idan kuka je saduwa a lokacin da kuke gabatar da wasannin (ROMANCES) a tsakanin ku, ka fahimce a wane wajen da wane wajen ne tafi jin dadi idan kana taba mata, idan ka lura da wannan sai karika amfani dashi ka kashe mata jiki a lokacin da kukaje saduwa.
Koda zaku fara saduwa takai mataki na 3 ko 4. Koda zaka kai matakin 6 ko 7 itama takai 7 kaga kenan kun kawo a tare😋😋😋😋.
Tohhhh ida zaku samu hakan sau daya a dare ko a sati kaiiiii koma a wata daya ne wallahi zaiyi wahala matar ka ta nemi wani na waje ko ta fada lesbianism kuma a hakan zaisa kaga dankon soyayya da tausayin juna ya karu a tsakanin ku..

5️⃣. Yazama wajibin Mutum namiji yakare kanshi yakare iyalansa daga wutar jahannama. Kamar yanda Allah (swat) yafada a cikin quran. Tabbas idan ka kasa ba matar ka abinci babanta na iya bata, idan kakasa mata sutura baban ta ko babanka ko yayanka ko kannen ka da sauran su suna iyayi mata dan a zauna auren, amma idan ka kasa a kwanciyar aure ba wanda ya isa yabata abunda take so a Shari'ah in ba kai ba saidai a raba Auren. 😭😭. Dan haka idan kanada yanda zakayi ka nemi ilimin jima'i ba haram bane, abu ne mai kyau kwarai da gaske a addinance, aladance da kuma Likitance.

6️⃣. Idan kuma kai kake da matsala a gefen mazakutar ka kamar rashin tashin mazakutar ka ko rashin sha'awa ko ciwon sanyi (INFECTIONS) ko ciwon sugar (DIABETES) ko saurin kawowa (PREMATURE EJACULATION) da sauran su, kaje asibiti kayi ma likita bayani zaiyima abunda yadace, kada ka tsaya wajen masu maganin gargajiya zasu halakar dakai a banza sucema sanyi ne su ko asiri ne etc....

CONCLUSION 
Wannann bayanin ya shafe MAZA kawai, kuma nayi bayanin ne tare da cikakken bincike akan abunda yashafi kwanciyar aure da kuma raayoyin wadanda abun yashafa.. Tare da binciken PSYCHOSOCIALOGIST akan jima'i da sauran su.

Nayi wannan bayanin ne A matsayi na na MAAIKACIN LAFIYA a gefen jinya (NURSING) domin ilmantar da jama'ah akan abunda yashafi SADUWAR AURE da dalilan dake sa matan Aure na neman mazan waje......

NAGODE

Post a Comment

0 Comments