ILLAR ISTIMNA'I GA MACE


ILLAR ISTIMNA'I GA MACE

 Rashin rike fitsari da kyau (ga mace) ko yawan zuwa fitsari saboda saka wani abu cikin farji lokacin istimna'i, wuyar kawowa ga mace wajen jima'i (dalilin koyama jikinta da sai an taɓa wani sashen farji don ta kawo, wanda mai yiwuwa ne zakari baya taɓa wurin lokacin saduwa - a zahirin jima'i. Don haka istimna'i yana sa rashin gamsuwar jima'i ga mace - mijinta zai sha wahala wajen gamsar da ita. Jikinta ya riga ya koya, tayima kanta horo. Dalilin haka, mace zata ji dadin istimna'i fiye da jima'i , hakan kuma zai zamo mata matsala idan tayi aure. Zata ringa tunanin mijinta baya iya gamsar da ita ko mazaje data aura, saboda sabon da tayi da koyama jikinta hanyar gamsar da kanta fiye da hanyar da ta dace, wato jima'i a cikin sunnar aure. Ta canza dabi'ar ta. Da yawa zaka samu cewa mata masu yawan istimna'i basu jin daɗin jima'i sai istimna'i, koma basu gamsuwa sai sunyi istimna'i a bandaki bayan saduwa da mazajen aurensu. Wannan zai iya kawo babbar matsala a cikin aure. Bugu da kari, dadilan rashin gamsuwar mace wajen saduwa da mijinta suna da yawa. Don haka, bazamu iya cewa ba yin istimna'i kafin aure shine dalilin dake hana gamsuwa kadai ba. Akwai wasu dalilan na daban, wasu matsalolin nada alaka da bangaren mazajen.

Mutumin da matsalar yawan wasa-da-al'aura ta zama dabi'arsa koda yaushe (addict) zaya iya maganin matsalar. Idan har yazama dabi'ar mutum baya jin dadin rayuwarsa sai yayi istimna'i (sau 2, 3, 4 ko fiye da haka a kowace rana) [addiction] toh zai iya kawo sauye-sauye (canje-canje) ga jikin mutum wanda lafiya bata maraba dasu ( such as hormonal imbalance), saboda yawan zubda sinadaran jikin mutum wajen inzali fiye dabi'ar jima'i ta gaskiya da sauyin yanayin jiki sakamakon yawan hakan . Yana da hadari ga lafiya yanda wasu matasa suka maida wannan dabi'arsu ta koda yaushe, a bandaki, a daki, a waje, ko a wurinda dama ba'a tsammani suna istimna'i..

To dole inde har kana so ka kawo sauyin da gaske to dole ka daure ka Bari.

Post a Comment

0 Comments