YAN MATA KU KULA!



YAN MATA KU KULA!

FAUZIYYA D SULEIMAN 💎 

Yan mata ku sani, wannan soyayyar da bin ki da saurayi ya ke yana lallashinki ba fa shi ake yi a gidan aure ba, akan samu masu yi din ko bai kai na waje ba amma ba su da yawa.

Don haka ki sani idan ki ka yi aure bautar Allah ce za ki yi, sai kin cire duk wani buri da hange-hange za ki samu zaman lafiya a gidanki, idan kuma ki ka yi hakuri watarana za ki girbi hakurinki, amma rudin kan ku da ku ke yi da tunanin za ku yi rayuwa kamar kuna aljanna ko ki ji dadi fiye da yadda ki ke ji a gidanku shine ya ke saka idan kuka yi auren kuke kasa samun kwanciyar hankali da nutsuwa, amma wadanda suka shiga babu mugun buri a ransu za ka ga suna zaune cikin kwanciyar hankali da hakuri domin sun san ibada ce.

Na yi wannan dan tsokacinne saboda yawan kira da na ke samu daga sabbin aure na korafi, idan na bincika kuma sai naga tun farko daukar aure da su ka yi a baibai shine ya janyo musu haka.

Abun da ya fi tayar min da hankali har na yi wannan dan rubutun shine, sakon da wata ta turo min wai wata shida da auranta kuma ta ji bata kaunar zaman auran, domin ita sabanin abun da ta ke zato ta gani, don haka tana neman na bata shawara tana son ta fito daga gidan mijinta, na yi mata nasiha da fada da bata misalin irin yadda muke zaune da hakuri da kawar da kai muma, musamman kuma da ta gaya min dalilinta, na wai mijinta bai damu ita ba kamar a baya ba, kuma idan ta ce ta ya mata abu sai ya ce ba shi da shi, sannan ko unguwa zata je sai ya ce ba shi da kudin motar da zai bata, sannan sai ya yi ta fushi yana shan kamshi duk soyayyar da ya ke mata a waje ya daina, ya mayar da ita kamar wata makiyiyarsa, abubuwa dai kala-kala da na gano ba wata babbar matsala ba ce na mata bayani sosai, domin na fuskanci a baibai ta fahimci aure, sannan ba ma zauna ta fahimci waye mijin na ta ba, irin rufa-rufar da muka saba yiwa juna lokacin neman aure har a gidan mijin haka suke yi da mijinta.
Wannan mau'du'in babba ne, idan na samu lokaci zan yi bayani dalla-dalla Insha Allah.
Amma daga karshe ina kira ga mata da ku sani, dole akwai bukatar yiwa miji biyayya sau da kafa don nima da girmana ina yi har gobe har jibi.
(Idan na sanu lokaci sosai zan yi karin bayani watakila har da vedios musamman ga wadanda suka shiga a matsayin second wife ko na uku ko hudu, don na su matsalolinma na neman fin yawa)

Post a Comment

0 Comments