LESBIAN!



LESBIAN!

Dear Sister 💕

Ke musulma ce? Kuma kinyi imani wata rana zaki farka a kabari? Kinyi imani wata rana Mala'iku zasu tayar dake suyi Miki tambaya akan ayyukan ki? 

Nasan ke macece mai hankali, nitsuwa da kamala. Ki kula kuma ki zauna kiyi tunani wallahi wannan abu yana da illa kuma kazanta ce. Saboda kazantarta ce masu yi basu bari a sani. Ki kula da duniya kafin ta kai ki ta baro ki. Rayuwan duniya ƙalilance akan na lahira. Allah ya yi miki niima, ya baki lafiya, hankali, ya suturta ki, ya baki ƴanci da ya yiki musulma, ta wanna hanyan zaki gode masa? 

Shin labarin mutanen Lud bai iso gareki ba? 
Waɗanda aka juya kasar su aka kife su, sannan aka musu ruwan duwatsu, sannan aka bar hakan ta zama iznā ga mu da muka zo bayansu? Kodai baki karanci tarihin su ba? Ko dai Qurani ba littafin Ubangijin ki bace? Ko dai kuma iƙrarin Musulunci neh a baka, amma zuciyar ki cike take da akasin haka?

Wallahi mutuwa tabbas ne, hisabi wajibi ne kuma wuta gaskiya ne. Ki tsare kan ki daga azaba mai tsanani da muni. 

Tarbiyya tayi mummunar lalacewa a wannan zamanin tamu, kuma dole a tashi a gyara, a dena kunyar kiran waɗan nan zuwa ga daidai, ko kuwa a haka zasu dinga jan kannenmu da ƴan uwanmu garesu, idan ba'a nuna hakan mummunan aiki bace, to da sannu shaiɗan zai ƙawata ta ta zam mai kyau. 

"Idan Masu Ilimi basu karantarba, da sannu wawaye da jahilai zasu yi tallar shashancin su" 

Wani Mawaki Yake Cewa: 

وغدا رويبضةٌ يُلَقِّنُ جَهْلَهُ
وربيبُ عِلْمٍ مُهْمَلًا مَنْسِيَّا

Ma'ana: 

Kuma Jahili yazo yana karantar da Jahilcin sa.

Mai ilimi kuma a manta dashi kuma a guje masa. 

Allah Ya mana shiriya, waye yafi kyawun zance, sama da wadda ke kira zuwa ga Allah, kuma ya aikata aikin kwarai, kuma yace; "Hakika Ni ina daga Musulmai", Hakika Aikin Kwarai bata daidaita da ta ɓata.❤️

 EEngr Ibrahim GudajiIEngr Ibrahim GudajiGEngr Ibrahim Gudaji

Post a Comment

0 Comments