Amfanin dabino ga lafiyar dan AdamDabino:


Amfanin dabino ga lafiyar dan Adam
Dabino:


Dabino nau’in dan itace ne da ake samun sa daga bishiyar dabino, wadda bishiya ce da aka fi samun ta a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ana samun bishiyar a yankin kasashen da ke gabar Teku, da nahiyar Asiya, da kuma Amurka da Mexico.

Dabino na fitowa a dunkule waje guda sakale a jikin bishiya. Yakan sauya launi zuwa uwan kasa, sannan ya motse yayin da ruwa yake fita daga cikinsa.

Hakan na afkuwa ne a lokacin da ake je cirarsa da hannu ta ko dai a sam wani ya hau bisiyar ko ta amfani da inji.



Amfanin dabino wajen gina jiki


Dabinon da ya bushe mai nauyin giram 30 na samar da:

81 kcal / 345KJ

Girma 1.0 na Abinci mai gina jiki

Giram 0.1 na ma su sa kiba

Girma 20.4 na abinci mai kara kuzari

Giram 20.4 na Suga

Giram 1.6 na nau'in narkar da abinci.

Giram 210 na sinadarin potashiyom


Bai wa jiki kariya

Dabino na da sinadarin da ke bai wa jiki kariya mai yawa.

Cikinsu akwai sinadaran polyphenols, da carotenoids, da lignans. Dukkansu sinadiran gina jiki ne da ke kare jikin ɗan Adam daga kamuwa daga cutuka masu tsanani.

Ƙara lafiyar ciki

Bincike kan abubuwan ci masu narkar da abinci na ci gaba da taka rawa mai mahimmanci ga lafiya, da taimakawa wajen tabbatar da lafiyar ciki, har ma da rage hadarin fama da cutuka masu tsayi.

Wani karamin bincike na 2015 ya gano cewa cin dabino zai iya rage kamuwa da ciwon kansa sakamakon sinadarin narkar da abinci na polyphenol, da amfanin da yake da shi wajen samar da sinadaren da ke taimakawa wajen kashe cutuka.

Ƙara lafiyar ƙashi

Dabino na da mahimmaci wajen kula da lafiyar ƙashi, saboda yadda yake dauke da sinadarin phosphorus, da potassium, da calcium da na magnesium.

Haka kuma dabino na da sinadarin karin lafiya na vitamin K da ke kara ƙarfin ƙashi.

Taimakawa wajen haihuwa cikin sauki

Cin dabino a makon karshe na mai ciki kafin haihuwa na taimakawa wajen rage tsayin naƙuda, sannan yana sa bakin mahaifa ya dinga budewa.

Haka kuma, ana kallon irin mahimmancin da suke da shi wajen takaita amfani aiki tsawon awanni.

Cikin sinadaran da dabino ya kunsa akwai oxytocin, wanda ke saukaka tsananin ciwon nakuda.

Ana Iya Amfani Da shi a Madadin Sukari

Ana shan ruwan dabinon bayan an jika shi a cikin ruwa.

Ruwan dabinon na da karancin sinadarin glycemic index (GI) da karancin sukarifiye da sauran na'ikan kayan zaki.

Shin kowa zai iya cin dabino?

Dabino na yi wa wasu mutane illa, kari kan haka wasu sinadarai da ake kira sulfites ka iya zama illa ga wasu mutane.

Ɗaya daga cikin illolin da dabino ka iya yi wa wasu mutanen shi ne kaikayin baki da na harshe, sai kuma atishawa da yoyon hanci.

Idan ka ga daya daga cikin irin wadannan alamu bayan cin dabino, ka tuntubi likita. Idan kuma an samu illa da ta fi haka, to a gaggauta zuwa asibiti

Post a Comment

0 Comments