Wasu Sakonnin Barka Da Asuba Da Zaki Iya Turawa Masoyinki:


Wasu Sakonnin Barka Da Asuba Da Zaki Iya Turawa Masoyinki:

#Tsangayarmalamtonga 
SHARE ⌚

Yiwa masoyi sakon barka da asuba yakan sa masoyi walwala da natsuwa. Irin Wadannan sakonnin sukan sa namiji ya wuni da tunanin masoyiyarsa.
Ga wasu sakonnin nan:

 
1: Da fatan masoyina ya tashi lafiya. Kada ka cika sugar a shayin da zaka sha gudun kada zakinka dana sugar su maka illa abun kaunata,. (Na matan aure ne).

2: Da zanyi arba da kai a wannan safiyar da zan rabu da ciwon idon rashin ganinka danake fama dashi.

3: Na kwanta da kewarka. Na kuma farka da soyayyar ka. Wannan yasa nake neman sanin yadda ka kwana ka tashi.

4: Babu abunda ke zuwa mini a rai sai daren karshe kamin kayi tayi. Da fatan ka tashi lafiya. (Na matan aure ne).
 
5: Da zaka karanci zuwaciyata, zaka fahimci ina tsananin tunaninka a wannan safiyar. Idan bazaka karanci zuciyata ba, ina fatan zaka karanta wannan sakon nawa na barka da asuba.

6: Hotonka dake bango dakin mu shine abunda idanuwana suka soma arba dasu a wannan safiyar. Hakan yake tuna mini irin sa'ar danyi cikin mata na samun miji Irinka. Barka da asuba. (Na matan aure ne).

7: Fadowa daga kan gado danayi shi yasa na fahimci gari ya waye. Sai dai faduwar tawa ya tabbatar mini da zamanka a birnin zuciyata. Da fatan ka tashi lafiya.

8: Gari ya waye, lokaci yayi da zaka tashi ka fuskanci nema bayan gaisawa da Allah (SWT). Kada kuma ka manta da masoyiyarka dake maka fatan Alheri ako da yaushe..

9: Ina kaunarka, amma kuma ina sonka, ina fatan kasancewa tare da kai har abada, ina burin ganin na zama uwar yaranka. Allah Ya bada sa'a idan an fita nema.

10: Ina kwana ga mutumin da yake na farko abun tunawa a zuciyata ako wace safiya. Kuma mai sani farin ciki ako wacce rana. 

 
Da fatan mata zasuyi amfani dasu domin sace zuciyar masoyansu.

Post a Comment

0 Comments