Yadda Ake Tafiyar Soyayya:


Yadda Ake Tafiyar Soyayya:


Daga amina yusuf gwamna 

 

Yadda ake tafiyar soyayya shi ne, ka yi kyakkyawan shiri don tarairaya, kulawa, da shagwaɓar amarya. Ita Wannan tafiya ana yin ta ne na kwanaki ko wuni guda. A tafi wani waje na Musamman. Wanda yake da dausayi. Akwai shuke-shuke, ruwa, dabbobi, ƙayatattun gine-gine da dai Sauransu.

Wasu na tafiyar soyayya da masoya ke yi, don nuna soyayya ga juna kwanakin farko da tarewarsu.

A wannan tafiya za su tsara rayuwar aurensu gaba ɗaya.

Amma fa ba sai sabon aure ba. Wannan tafiya na da muhimmacin gaske ga tsofaffin ma’aurata. Sai a kai yara gidan kakanninsu su zauna. Ko kakarsu ta zo ta zauna da su kafin ku dawo.

Ga tsofaffin Ma’aurata ita ce keɓantacciyar tafiya da waɗanda suka yi auren soyayya ke yi, don samun keɓewa, sakewa, nishaɗi da jin daɗi.

A irin wannan tafiyar ce, za su sami damar gyara soyayya, duk yar wata rashin jituwa, ko kura-kuren da aka yi wa juna. Wato tafiya ce ta sabunta soyayyya.

Ga wanda ba su da lokacin yin kwanaki. To sai su dinga tattalin ranakun hutun aiki (weekends) .Wajen yini cur a wuraren shaƙatawa. Ko da kuwa lambu, gidan Dabbobi (zoo), ko Minjibir Park, Kano.

MATAKAI NA TAFIYAR SOYAYYA.

1- Na farko ya zama akwai kyakkyawar niyya ta ƙarfafa soyayya .

2- A tattauna tare Ango da Amarya. Ko Maigida da Uwargida kan zaɓar lokaci da wurin da za a je.

3- Ango/Maigida ya yi aski. Ya zabi kayan ado masu kyau, da turare don mallake zuciyar masoyiyarsa.

4- Amarya/Uwargida ta yi gyaran jiki, ƙunshi, da gyaran gashi. Ta ɗauki turare da humra.

5- Ango/ Maigida zai tanadi kuɗi wadatattu. Don biyan ɗakin kwana, abinci, kayan marmari da zuwa wuraren ziyara.

6- Inda hali ana iya tanadar wa juna Kyautar bazata.

7- Ma’aurata su saki ransu. Cin abinci, wanka, tsere, rawa da wasanni tare.

Ba shakka duk Ma’aurata dake irin Wannan tafiyar soyayya . Su Ka bi waɗannan matakai na yadda ake tafiyar soyayya .

 Za ka ga rayuwarsu na cike da tsantsar soyayya da begen juna.
.

Post a Comment

0 Comments