Yadda Ake Gyaran Jiki Yai Laushi Kuma Yai Kyau:
Daga amina yusuf gwamna
Yadda Ake Gyaran Jiki Yai Laushi Kuma Yai Kyau: Gyaran jiki yana taimaka wa Namiji ko Mace ta daɗe tana more jikinta. Fatar mutum ta zama lafiyayya, kuma abin sha’awa. Shi ne za ka ga mace komai yawan shekarunta, haka komai yawan haihuwarta, Tana da kyakkyawan jiki.
Gyaran jiki ya samo asali ne daga wajen Larabawa. Sai Barebari wato daga Maiduguri, a nan Ƙasar NIjeriya. Haka ma Turawa sun yi mayuka kala-kala domin gyara fata.
Sai dai duk Sanda mutum yake so zai dinga gyara jiki. To ya zama tilas ya kula da mafi muhimmanci, wato ya bi matakai na gyara jiki.
MATAKAI NA GYARAN JIKI:
1 – Cin lafiyyen abinci.
2 – Yawan Shan ruwa .
3 – Yawan Cin ‘ya’yan itatuwa.
4 – Atisaye ( motsa jiki) .
5 – Amfani da kayan gyaran jiki ( Dilka).
GYARAN JIKI NA DILKA:
Za a zuba Dilka a cikin mazubi. Sai a zuba masa ruwan zafi. Bayan jimawa sai a zuba kurkum, da mai zaitun , da ƙwai .
Sai a ƙara ruwa ɗan daidai. A shafe dukkan jiki har fuska. Idan ya bushe sai a murje jiki da shi.
GYARAN JIKI NA ALKAMA:
Za a nika Alkama ne, a tankaɗe ta, tai lukwui. Sai a soya ta kamar yadda ake idan za a yi kunun alkama.
Za a zuba wa soyayyiyar alkama yis. A zuba ruwa a kwaɓa ta. A shafe duk jiki da ita. Bayan ɗan lokaci, sai a dinga murje jiki ko’ina.
GYARAN JIKI NA KHALDA ( OATS):
Za a zuba wa khalda (Oats) madara. Sai kuma a matsa lemon tsami kadan. A juya shi a kwaɓa sosai. Sai a shafa amma shi duk jiki. Bayan ɗan lokaci sai a murje duk jiki.
A ƙarshe, lallai akwai buƙatar mu dinga waiwayar gyaran jikinmu, duk sati in da hali. Ko kuma duk Wata. Ya danganta da yadda ake da hali, lokaci da himma.
Duba yadda ake ado da kwalliya ta Musamman.
Litattafai da aka duba
Amina Mar’atussaliha
0 Comments