YADDA AKE GYARA SOYAYYA:



YADDA AKE GYARA SOYAYYA:

Ana gyara soyayya ne ta fahimtar ma’anar so, zuciya, alamomin soyayya, rabe-raben soyayya da dai Sauransu .

Da farko mu fahimci So ko ƙauna shi ne yarda da amincewar zuciya game da wani mutum ko wani abu.

A gyaran soyayya sai mun fahimci matsayin zuciya. Zuciya ita ce inda so ko ƙauna ke zaune. Zuciya kuwa babu wani da yake da iko da ita sai Allah (SWT) da ya halicce ta. Allah shi yake kimsa so a cikin zukata. A wajen gyara soyayya sai mutum yai shirin shiga kogin da ba a fitowa.

 Soyayya wani kogi ne wanda duk ya faɗa cikinsa, sai yai ninƙaya ya kasa fita.

Son da zukata guda biyu ke wa junansu, shi ake kira soyayya. Takan zama soyayya mai ƙarfi ko mai rauni.

Mai gyaran soyayya sai ya koyi Ingantacciyar soyayya. Saboda Ingantacciyar soyayya ko ƙauna tana dauwama a zukata ne har abada.
Tabbas So ya faranta wa mutane da yawa. Kuma so ya wahalar da mutane da yawa. Babu wanda ya kuɓuta daga tasirinsa. Kun ga kenan tilas mu duba yadda za mu yi gyara a soyayya.

A ɗan taƙaice, kafin mu je hanyoyin da za a gyara soyayya. Ya kamata mu yi nazari a abin dake kawo matsalolin da muke samu a soyayya ko ince ƙauna.

Ƙauna ta gaskiya ba ta ƙarewa, sai dai takan iya sanyi saboda nisa, rashin samun kulawa, ƙiyayya daga ɗaya ɓangaren ko rabuwa.

In kuwa ka ji an ce maka ta ƙare, to dama sha’awa ce, ko kwaɗayin samun dukiya, mulki da dai sauran su.

Shi So yana da wahala ka iya cire shi in har ya shige ka. Masoya na haƙiƙa sun yi bayani su na iya haƙura da abubuwa da yawa a rayuwa, amma ban da son masoyansu.

HANYOYIN DA ZA A GYARA SOYAYYA SU NE :
1- Soyayya ta zama an gina ta a kan gaskiya. Ka da a shigo da yaudara. Misali mace ta dinga ƙarin gashi, ƙirji , ko canja launin fatar jiki. Namiji ma ya kiyaye aron Riga, mota, ko kuɗi.

2- Soyayya ta zama mafi tsarki. Wadda Babu taɓa jikin juna, zantukan batsa, Balle saɓon Allah.

3- Soyayya ta zama ana bayyana ta. Bayyana wa Masoyi/Masoyiya irin son da ake ji. Cikin kalmomin girmamawa da ƙauna.

4- Soyayya ta zama ana yawan tuntuɓar juna. Damuwa da halin wanda ake so yake ciki.

5-Soyayya ta zama ana amfani da hanyoyin zamani na waya da yanar gizo. Aikawa Masoyi/Masoyiya Sakonnin hotunan furanni, zuciya da kalmomin soyayya. Bidiyo waƙoƙin soyayya don gyara soyayya.

6- Soyayya ta zama ana karɓar gyara. Kuma ana afuwa ga wanda ake so. Banda mita da riƙo.

7- Soyayya ta zama ana ƙoƙarin farantawa da kyautatawa. Tare da bada Kyauta. Kyautar katinan soyayya, turare, agogo, zobe, da dai Sauran su.

8- Soyayya ta zama akwai kunya. Ita kunya ado ce a soyayya , alkhairi ce, tana gyara soyayya.

9- Soyayya ta zama ana koyi da Annabi (S.A.W) . Muna da kyawawan misalai da yawa daga gidan Annabi (SAW) da iyalansa.

10- Soyayya ta zama ana neman ilminta ( karatu) . Tare da karance-karancen labaran masoya.

A taƙaice, bibiyar waɗannan hanyoyin zai kawo mana gyara a cikin soyayya. Duba da muhimmancin soyayya a cikin rayuwarmu.
A soyayya ba talaka, ba shugaba, ba mai kuɗi. Za ka samu mafi yawan hazuƙan mutane sun so wata mace a rayuwarsu. Wasu Malamai, Shugabanni, Sarakuna da dai Sauransu. Saboda muhimmancinta ya zama tilas mu san hanyoyin yadda za mu yi gyara a soyayya.

Post a Comment

0 Comments