#SAMARIN #ZAMANI:
idan mukace samarin zamani muna nufin samari masu hana #AURE:
zamu kawo misalinsu dan aganesu da kamannisu.
Samari zamani sun kware wajen iya yaudara da satar zuciya gashi sun iya salo daban-daban.
kai wasuma har majalisa kegaresu wato inda suke zama suna gasar Yaudara, ga iya magana da budurwa cikin murya mai sanyi, zaka ga sunrike manya wayoyi a hannu,anakara kidin mota dazaran yasamu dammar yi maki magana shikenan yasamu hanyar kabar lambar wayarki,kina bashi lambar zai ce sorry baby a cikin zuciyarsa,kekam taki ta kare.
daga nan zaki fara ganin jerin waya akai-akai da kalamai masu ratsa zuciya sannan kuma zai rinka nuna maki tsantsar soyayya,ga yawan text masu dadi:
❝ zai rinka nuna maki cewashi zai iya mutuwa idan bai aurekiba.
ko yace maki zai iya shiga wani hali idan bai aurekiba.
❝ ko yace maki ya kasa bacci saboda ke.
❝ ko yace rashin ganinki ya sashi rashin lafiya.
haka dai zaita shirya maki gadar zare kina hawa shikenan yagama dake sai dai wata kuma bakeba.
Saboda haka shi saurayin zamani ba zai bayyana maki manufarsa dawuriba sai kingama bashi amana.
❝ kingama yarda dashi,kingama bashi soyayyarki yanata nuna maki shifa aure kawai yakeso kekuma kinata murna kinsamu mijin aure.
kai wanima har sai yaje gidanku ya gaida iyayenki suma suyita murna wance tayi sa'a shi kuma yana zuwa majalisa sai labari yana cewa zan yi maganinta, sai kinyi nisa cikin duniyar soyayya dashi, daya samu yabiya bukatarsa dake zai ce nayi maganinta,saboda ya fanshe wahalar da yayi maki kuma daga ranar daya samu ya biya bukatarsa shikenan kuma baki qara gane kansa, daganan kuma kina wucewa sai yaita bada labarinki yana cewa akwaita da hankali shi kuma yana cewa 'yar isaka ce, kaza da kaza nayi da itadaga nan kuma zaki ga yarage kiranki a waya, kuma zai rage zuwa gidanku, kina ce masa zakazo yana cewa ai wani aiki aka sani kokuma kina kiranshi a waya baya dauka,koma ya kashe wayar ko yace maki zani kiraki inagama aikin daganan bazai kiraba kuma zai rahe yimaki hidima kina ce masa kwana biyu baka zoba lafiya?
Ko namaka laifine shi kuma yana ce maki nayi tafiya ne, sai randa babu wurin zuwa sai yazo,kina ce masa to gidafa sun matsa ka turo,shi kuma sai kiji yace dady yaje umra,bayan wadansu kwanuka yace maki ai ya dawo munyi magana yace zai nemi yayanshi haka dai zai ta wasa da hankalinki kai wanima har sai yasa rana kinsanarda iyayenki,ranar tana zuwa sai kiji yace anyi masa rasuwa,babanmu yaje kauye saboda kanwarsa ceta rasu,kinga yasa kinyiwa iyayenki karya,kina ganin kinyi sa'a amma kuma akasin haka har ila yau bayan wani lokaci idan kika sake yi mashi magana sai yace wallahi mama tace bata yardaba nayi iya kokarina wurin fahimtarda ita da bata hakuri amma ina taki fahimta,wai tanaso ta hadani da wata yar'uwata ne,ni kuma bana sonta,wani saurayin kuma zai iya turo wadansu mutanen a matsayin iyayensa ko ya kawo goron gaisuwa don yaudara,saboda ki bashi hadin kai,wani kuma yace ina gini ne saboda bana son zama a gidan haya, zaima iya nuna maki wani gida na wani da ake ginawa ya nuna maki yace nanne ginin da nakeyi,ko yace maki yan'uwana basa son nayi aure har sai nagama karatuna, kokuma yace maki kishiyar mamarsa tayi masa asiri sai abunda tace a gida ake bi,wani kuma yace shi da kansa ne akayi masa sihiri,kokuma yace anyi masa satar kudi wani kuma harma sai yasa kinyi lissafin kudin kayan auren ko kuma ya hada kai da wani mai shago,dama abokinsane sai ya karbi kayan ya kai gida, kina murna sai kawai yazo yace maki ansace kayan,sai ya maidawa abokinnasa kayansa Allah sarki! Wani kuma hada baki zai yi da abokinsa don yazo wurinki fira,sai kuna cikin fira kawai sai yazo,yana ganinku sai yayi fushi mai tsanani sosai domin yanason ya samu hanyar rabuwa dake tunda ya riga ya yaudareki,ya san komai naki shikenan sai ya gudu ya barki da kuka, abun haushima idan kinyi aure me zaki fadawa mijinki na #SUNNAH, kice masa antaba yi maki fyade ne? Ko zakiyi shiru ne don kina ganin bazai ganeba? Ai masu magana suna cewa idan aka bude maltina tag wan-gwani ya za'ayi a rufeta dai-dai? Bazai yiwuba, shikuma yana cen ko a jikinsa,sai dai kiji ana cewa zuwa yawo aita auri wane,har idan kika haihu da yaranki sun wuce sai a rinka nunasu,haka dai ba girma #YAN MATA
0 Comments