بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
YADDA AKE WANKAN JANABA
Daga Islamic Best
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai
ﻭَﺻَﻠَﻰ ﺍَﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﻦْ ﻵ ﻧَﺒِﻲِّ ﺑَﻌْﺪَﻩُ
Tsira da amincin ALLAH sutabbata ga ANNABIN dababu wani bayanshi
Salati da tsira da amincin Allah su tabbata bisa Jagoran Annabawa da Manzanni, Shugabanmu Annabi Muhammadu (ﷺ) tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa Maɗukaka.
قال اللّٰه تعالى: : (وَإِن كُنتُمۡ جُنُبا فَٱطَّهَّرُواْۚ) [المائدة: 6]
Allah Maɗaukakin Sarki ya ce,“Idan kun kasance kuna da janaba to ku yi wanka” (Alma’ida : 6)
ولقوله (ﷺ) لعلي رصى الله عنه: «فَإِذَا فَضَخْتَ الْمَاءَ فَاغْتَسِلْ» (رواه أبو داود
da faɗin Manzon Allah (ﷺ) ga Aliyyu : “Idan ka fitar da ruwa to ka yi wanka” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].
Siffar Wankan Manzon Allah (ﷺ)
حَدَّثَنِي يَحْيَى عَنْ مَالِكٍ عَنْ هِشَامِ بْنِ عُرْوَةَ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ الْمُؤْمِنِينَ أَنَّرَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ إِذَا اغْتَسَلَ مِنَ الْجَنَابَةِ بَدَأَ بِغَسْلِ يَدَيْهِ ثُمَّ تَوَضَّأَ كَمَا يَتَوَضَّأُ لِلصَّلاَةِ ثُمَّ يُدْخِلُ أَصَابِعَهُ فِي الْمَاءِ فَيُخَلِّلُ بِهَا أُصُولَ شَعْرِهِ ثُمَّ يَصُبُّ عَلَى رَأْسِهِ ثَلاَثَ غَرَفَاتٍ بِيَدَيْهِ ثُمَّ يُفِيضُ الْمَاءَ عَلَى جِلْدِهِ كُلِّهِ.
Advertisements
REPORT THIS AD
Yahayya yabani labari daga Maliki daga Hisham ɗan Urwa daga babansa daga A’isha uwar muminai cewa Manzon Allah (ﷺ) ya kasance idan zaiyi wankan janaba yana farawa da wanke hannayensa sannan saiyayi alwala kamar yadda yake alwalar sallah sannan sai yashigar da hannayensa cikin ruwa sai yajiqa asalin gashinsa sannan yazuba kamfata ukku ruwa akansa da hannayensa sannan ya kwarara ruwa akan fatarsa dukkansa. (Muwaɗɗa)
حدثنا يوسف بن عيسى قال أخبرنا الفضل بن موسى قال أخبرنا الأعمش عن سالم عن كريب مولى ابن عباس عن ابن عباس عن مَيْمُونَة -رضي الله عنها- قالت: «وَضَعَ رَسُولُ اللهِ (ﷺ) وَضُوءًا لِجَنَابَةٍ، فَأَكْفَأَ بِيَمِينِهِ عَلَى شِمَالِهِ مَرَّتَيْنِ أَوْ ثَلَاثًا، ثُمَّ غَسَلَ فَرْجَهُ، ثُمَّ ضَرَبَ يَدَهُ بِالْأَرْضِ أَوْ الْحَائِطِ مَرَّتَيْنِ أَوْ ثَلَاثًا، ثُمَّ مَضْمَضَ وَاسْتَنْشَقَ، وَغَسَلَ وَجْهَهُ وَذِرَاعَيْهِ، ثُمَّ أَفَاضَ عَلَى رَأْسِهِ الْمَاءَ، ثُمَّ غَسَلَ جَسَدَهُ، ثُمَّ تَنَحَّى فَغَسَلَ رِجْلَيْهِ، قَالَتْ: فَأَتَيْتُهُ بِخِرْقَةٍ فَلَمْ يُرِدْهَا، فَجَعَلَ يَنْفُضُ بِيَدِهِ» (رواه البخاري
Yusufa ɗan asi ya bani labari yace fadalu ɗan musa ya ba mu labari yace A’amash ya ba mu labari daga sãlim daga karib ‘yantaccen bawan ɗan Abbas daga Abbas daga Maimunatu uwar muminai Allah yayarda da ita, ta ce, “Manzon Allah (ﷺ) ya sanya ruwa don yin wankan janaba, sai ya karkato abin ruwan da hannun damansa a kan hagunsa ya wanke hannayensa sau biyu ko sau uku, sannan ya wanke gabansa, sai ya doki qasa ko bango da hannunsa sau biyu ko sau uku, sannan sai ya yi kurkurar baki ya shaqa ruwa, ya wanke fuskarsa da sangalin hannunsa, sannan ya kwara ruwa a kansa, sai ya wanke jikinsa, sannan ya matsa gefe guda ya wanke qafafunsa. Nana Maimunatu ta ce, “Sai na kawo masa wani qyalle (hankici) amma bai karɓa ba, sai ya riqa share ruwan da hannunsa” [Bukhari ne ya rawaito shi].
daga cikin waɗannan wankan duk wanda aka ɗauka yayi saboda abinda ake nufi da wanka game jiki daruwa.
Yaya Mace zatayi a wankan janaba?
وَحَدَّثَنِي عَنْ مَالِكٍ أَنَّهُ بَلَغَهُ أَنَّ عَائِشَةَ سُئِلَتْ عَنْ غُسْلِ الْمَرْأَةِ مِنَ الْجَنَابَةِ فَقَالَتْ لِتَحْفِنْ عَلَى رَأْسِهَا ثَلاَثَ حَفَنَاتٍ مِنَ الْمَاءِ وَلْتَضْغَثْ رَأْسَهَا بِيَدَيْهَا.
(Yahayya laisi yace) Maliki yabani labar cewa shi labari ya isheshi cewa A’isha
Allah Ya yarda da ita an tambayeta game da wankan macce daga janaba sai tace “Ta zuba ruwa akanta zubawa ukku sai ta cuɗa kanta da hannunta” @malik muwaɗɗa
وَعَنْ أُمِّ سَلَمَةَ رَضِيَ اَللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ: «قُلْتُ: يَا رَسُولَ اَللَّهِ إِنِّي اِمْرَأَةٌ أَشُدُّ شَعْرَ رَأْسِي, أَفَأَنْقُضُهُ لِغُسْلِ اَلْجَنَابَةِ؟ وَفِي رِوَايَةٍ: وَالْحَيْضَةِ؟ فَقَالَ: “لَا، إِنَّمَا يَكْفِيكِ أَنْ تَحْثِي عَلَى رَأْسِكِ ثَلَاثَ حَثَيَاتٍ”» رَوَاهُ مُسْلِمٌ
An karɓo daga Ummu Salma Allah Ya yarda da ita ta ce: “Na ce: Ya Manzon Allah! Ni mace ce, da nake kitsa gashin kaina, shin ko na warware shi, saboda wankan janaba?. Kuma a cikin wanin ruwayan, cewa: Da Jinin haila. Sai ya ce: A’a, kaɗai ya ishemiki zuba tafi uku na ruwa akanki.” Muslim ne ya ruwaito shi.
YADDA AKE WANKAN JANABAR
: Tun farko dai mutum zai yi niyya, niyya kuwa tana farawa ne tun daga sanda ka ɗauki ruwanka mai Tsarki.
: Sannan zaka sami ruwa mai tsarki, idan abin da ruwan yake ciki buɗaɗɗene sai a sashi a bangaren hannunka na dama, idan kuma rufaffene sai sashi a hannun hagu(kamar buta).
: Sai a fara da sunan Allah wato BISMILLAH (amma a zuci, saboda ba a ambaton sunan Allah a yayin da ake cikin banɗaki). Sannan a wanke hannu kafin a fara komai.
: Sannan sai ayi tsarki (da wankewar gaba da kuma kewayensa).
: Bayan wannan sai ayi alwala shuɗi dai-dai, idan anga a jinkirta wankin kafafu sai a karshen wanka.(amma malamai sunce an hana barin sunna a cikin yin wanka, barin sunna makaruhi ne, an qishi ana so musulmi yayi wanka cikakke tare da farillan wanka da kuma sunnonshi). Kun ga kenan alwalar mu zamu yi ta ne cikakkiya kamar zamu yi Sallah.
: Sannan a wanke kai sau uku, za a shigar har da wuya a wankin kai, da wankin kunnuwa ciki da waje, mace kuma zata zuba ruwa a cikin gashinta ta bubbuga sai ruwan ya shiga ciki sosai. Amma idan tana da larura to anso ta shafa kanta sau ukun ko ina da ina.
: Sannan a wanke tsagin jiki na dama tun daga kafaɗa har zuwa qafa, sannan a wanke tsagin jiki na hagu shima tun daga kafaɗa harqafa. a cuccuda sosai da sosai.
: Sannan sai a game jiki da ruwa.
TUNATARWA:
Ana so ko ina ya shafi ruwa kamar su matsematsi cinyoyi, da kuma kwarin cibiya duk a tabbatar an cuɗa su da kyau. Sannan a kula kada a shafi Al’aura. Domin aka shafi al’aura alwala ta karye.
Abubuwan dake wajaba a wanka
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ اَلْخُدْرِيِّ - رضى الله عنه - قَالَ: قَالَ رَسُولُ اَللَّهِ (ﷺ)«اَلْمَاءُ مِنْ اَلْمَاءِ» رَوَاهُ مُسْلِمٌ.
An karɓo daga Abi Sa’idil Khudiri Allah Ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ana taɓa ruwa ne saboda fitar ruwa” Muslim ya ruwaito shi
وَعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ - رضى الله عنه - قَالَ: قَالَ رَسُولُ اَللَّهِ - (ﷺ) «إِذَا جَلَسَ بَيْنَ شُعَبِهَا اَلْأَرْبَعِ ثُمَّ جَهَدَهَا فَقَدْ وَجَبَ اَلْغُسْلُ» مُتَّفَقٌ عَلَيْهِ
An karɓo daga Abi Huraira Allah Ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan ɗayanku ya zauna a tsakanin cinyoyi hudu yayi ƙoƙarin jima’i, to, wanka ya wajaba.” Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.
زَادَ مُسْلِمٌ: “وَإِنْ لَمْ يُنْزِلْ”
Muslim ya ƙara cewa: “Koda baiyi maniyyi ba.”
وَعَنْ أُمِّ سَلَمَةَ أَنَّ أُمَّ سُلَيْمٍ -وَهِيَ اِمْرَأَةُ أَبِي طَلْحَةَ- قَالَتْ: «يَا رَسُولَ اَللَّهِ! إِنَّ اَللَّهَ لَا يَسْتَحِي مِنْ اَلْحَقِّ, فَهَلْ عَلَى اَلْمَرْأَةِ اَلْغُسْلُ إِذَا اِحْتَلَمَتْ؟ قَالَ: “نَعَمْ. إِذَا رَأَتِ الْمَاءَ”» اَلْحَدِيثَ. مُتَّفَقٌ عَلَيْهِ
An karɓo daga Ummi salamata cewa ummi sulaimin ita matar abi ɗalhatane tace: “Ya Manzon Allah (ﷺ) lallai Allah bayajin kunyar gaskiya, shin akwai wanka ga mace idan tayi mafarki? yace: “E” idan taga ruwa.” hadisin bukhari da musulim suka ruwaitoshi
وَعَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ - رضى الله عنه - قَالَ: «قَالَ رَسُولُ اَللَّهِ (ﷺ) فِي اَلْمَرْأَةِ تَرَى فِي مَنَامِهَا مَا يَرَى اَلرَّجُلُ- قَالَ: “تَغْتَسِلُ”» مُتَّفَقٌ عَلَيْهِ.
An karɓo daga Anas ɗan malik Allah Ya yarda da shi ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: A game da macen da take gani a cikin barcinta da abin da (mutum) namiji yake gani, (na mafarki)? Sai ya ce: Sai tayi wanka.” Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.
وَعَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اَللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ: «كَانَ اَلنَّبِيَّ (ﷺ) يَغْتَسِلُ مِنْ أَرْبَعٍ: مِنْ اَلْجَنَابَةِ، وَيَوْمَ اَلْجُمُعَةِ، وَمِنْ اَلْحِجَامَةِ، وَمِنْ غُسْلِ اَلْمَيِّتِ» رَوَاهُ أَبُو دَاوُدَ, وَصَحَّحَهُ اِبْنُ خُزَيْمَةَ.
An karɓo daga Aishatu Allah Ya yarda da ita ta ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya kasance yana yin wanka ga abubuwa huɗu (sune) na yin janaba, kuma da ranar Juma’a, kuma da yin ƙaho. Kuma daga yin wanka ga mamaci.”Kuma Abu Dawud ne ya ruwaito shi. Kuma ɗan Khuzaima ya inganta shi.
ko shin ya halatta mai janaba ko haila su shiga masallaci
وَعَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اَللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ: قَالَ رَسُولُ اَللَّهِ (ﷺ) «إِنِّي لَا أُحِلُّ اَلْمَسْجِدَ لِحَائِضٍ وَلَا جُنُبٌ» رَوَاهُ أَبُو دَاوُدَ وَصَحَّحَهُ اِبْنُ خُزَيْمَةَ.
An karɓo daga Aisha Allah Ya yarda da ita ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ni bani halatta masallaci ga mai haila, da mai janaba ba.” Abu Dawuda ya ruwaito shi, ɗan Khuzaima ya inganta shi.
wannan daga littafin kawa’idi
Abubuwan dake wajaba a wanka
بَـــابُ مُوجِبَاتِ الْغُسْلِ:
BABIN ABUBUWAN DA SUKE WAJABTA WANKA
وَأَمَّا مُوجِبَاتُ الْغُسْلِ فَأَرْبَعٌ:
amma abubuwan da suke wajabta wanka guda huɗu ne
خُرُوجُ الْمَنِيِّ بِلَذَّةٍ مُعْتَادَةٍ فِي نَوْمٍ أَوْ يَقْظَةٍ، أَوْ مُغِيبُ حَشْفَةِ بَالِغٍ فِي فَرْجٍ،
Futowar Maniyyi domin jin daɗi na al’ada a barci ko a farke
Ko ɓoyuwar hashafa (kaciyar) baligi a cikin farji,
أَوِ انْقِطَاعِ دَمِ الْحَيْضِ أَوِ انْقِطَاعِ دَمِ النِّفَاسِ، وَإِسْلاَمُ الْكَافِرِ.
Yankewar jinin haila ko yankewar jinin nifasi
musluntar Kafiri
اِنْتَهَى مُوجِبَاتُ الْغُسْلِ
Abubuwan da suke wajabta wanka sun tuke.
Babin wanka na sunna
بَـــابٌ فِي الْغُسْلِ الْمَسْنُونِ
BABIN WANKA ABIN SUNNANTAWA
وَأَمَّا الْغُسْلُ الْمَسْنُونُ فَسَبْعٌ:
amma wanka abin sunnantawa guda bakwai ne
غُسْلٌ لِصَلاَةِ الْعِيدَيْنِ، وَغُسْلُ صَلاَةِ الْجُمُعَةِ، وَغُسْلٌ لِدُخُولِ مَكَّةَ،
Wankan Sallar Idi biyu, da Wankan Sallar Juma’a, da Wankan shiga Makka,
وَغُسْلُ الْمَيِّتِ، وَغُسْلُ دَمِ اْلإِسْتِحَاضَةِ إِذَا انْقَطَعَ،
da Wankan matacce, Wankan jinin da yake zowa mace domin rashin lafiya idan ya ɗauke,
وَغُسْلٌ لِصَلاَةِ خُسُوفِ الشَّمْسِ، وَغُسْلٌ لِصَلاَةِ اْلإِسْتِسْقَاءِ سُنَّةٌ،
اِنْتَهَى الْغُسْلُ الْمَسْنُونُ.
da Wankan Sallar kisfewar rana,
da Wankan sallar rokon ruwa,
Wanka abin sunnantawa sun tuke anan.
0 Comments