NAU'IKAN ABINCIN DA SUKE GYARA MAZANTAKAR MUTUM:



NAU'IKAN ABINCIN DA SUKE GYARA MAZANTAKAR MUTUM

1. QARA RUWAN MANIYI

A. Tafarnuwa (Garlic): A cikin duk abincin da mutum yake ci, babu wadda yakai tafarnuwa qara ruwan maniyi.
B. Ayaba (Banana): Banana tana dauke da sinadarin qara ruwan maniyi. Tana daga cikin manyan abincin da mutum Namiji ya kamata ya yawaita ci domin neman ruwan maniyi
C. Kifi: Kifi yana cikin jerin manyan abubuwan da suke qara ruwan maniyi da kuma saurin tashin gaba.
D. Madara: Madara ma tana ciki, amma bata kai kifi da tafarnuwa da kuma Ayaba saurin qara ruwan maniyi ba. Amma dai ita ma tana daga ciki.
E. Piya (Avocado): Avocado yana dauke da sinadarin Protein sosai. Dan haka aikin sa yana qara kuzari ne a jikin dan adam, sannan kuma shima yana qara ruwan maniyi, saidai shima qarawar sa kamar Madara ne, ma'ana bai kai su tafarnuwa da kifi da Ayaba saurin qarawa ba, amma itama ana so mutun ya yawaita ci

QARA QARFIN GABA:

A. Tattasai: Tattasai yana daya daga cikin abubuwan da ake so duk Namiji ya jingina wa kansa yawan ci. Saboda tattasai ya fi komai qara qarfin gaba. Shi tattasai baya qara ruwan maniyi. Kar kayi tunanin idan kana cinsa zai qara maka ruwa, a'a, aikin sa yana qara qarfin gaba ne.

B. RAKE (Sugarcane): Kasancewar Rake yana daga cikin abubuwan da suka fi komai Glucose. Rake yana qarawa Namiji kuzari fiye da yadda mutum yake tunani wajen yin Jima'i.

C. Gyada (Groundnut): Gyada tana da protein. Aikin ta kamar na Piya ne. Tana matuqar qarawa Namiji kuzari sosai. Sannan yawan cin gyada zai sa kaji baka gaji da Jima'i da wuri ba. Ana so namiji ya jingina wa kansa yawan cin gyada.
D. Albasa (Onion): Albasa tana qara ruwan maniyi, amma ba sosai ba. Dan wasu ma suna ganin kamar a cire ta daga cikin jerin abubuwan da suke qara ruwan maniyi, saboda ba kamar sauran take ba. Ita albasa aikin ta shine, tana qara GIRMAN azzakari ne, musamman idan kana cinta da 'Danyen qwai.

Wadannan abubuwan da na lissafa, haqiqa idan ka yawaita cin su, wallahi kai da kanka zaka tabbatar da chanjin da kake ji a jikin ka. Musammam idan kayi sati kana cin su, kuma a cikin satin nan baka sadu da matar ka ko sau daya ba, ma'ana ka shiga hutun yin Jima'i domin ka samu ka ci wadannan abubuwan yadda ya kamata. To haqiqa duk ranar da ka kusanci matar ka, lalle zata gane cewa Oga ya yi service din engine din sa.

SHAWARA: Ana so mutumin da bashi da aure ya nesanta kansa da cin wadannan abubuwan da aka lissafa a farko. (Ina magana akan abincin da suke qara ruwan maniyi, ba wadanda suke qasa kuzari ba). A lura, wadannan abubuwa ne guda biyu mabanbanta.

Dalili kuwa shine, idan ruwan maniyi yayi kaka yawa, kuma bakka da inda zaka rubar dashi (ma'ana baka da aure), to tabbar zaka fiskancin qunci!
Amma idan ka yawaita cin abubuwan da suke qara qarfin gaba da sauran su, kamar su gyada, albasa da tattasai, to wannan babu matsala.

Sai magana akan Aya (Tiger nut).
Da yawa mutane sun yiwa Aya mummunar Fahimta. Sun dauka cewa daga mutum ya ci Aya, ko kuma ya sha kunun Aya, to shikenan cikin qanqanin lokaci sai komai ya chanza. Maganar gaskia wannan chanfi ne kawai.

Gaskiar magana akan Aya shine, a research din da nayi, na samu cikakken Bayanin cewa, ita aya sai ka jera kwanaki ashirin da uku kana cinta kullum babu qaqqautawa, to a nan ne zata fara aikin ta. Aikin ta kuma shine, tana qara girman gaba, tana sanya sha'awa mai yawa, tana qara ruwan maniyi, sannan tana sanya kuzari (kamar yadda Rake yake yi).

Wannan bayani ne da ya shafi Maza zallah. Insha Allahu next rubutu na zan yi shi ne akan Abincin da mata ya kamata su dinga ci, da kuma me yake qara musu, amma ban gama bincike akai ba.

Kema 'yan uwa idan kina son jin dadin rayuwar ki, to ki sanya mijin ki ya dinga yawan cij wadannan abubuwan da na lissafa. Insha Allahu bazai nemi maganganun qara MAZANTAKAR MUTUM ba.

Daga naku AbdulHadi Abba Kyari (Kuyi searching dina kuyi adding dina as friend)


Post a Comment

0 Comments