*IYALINKA SIRRINKA NE*
_______ ★ _________ ★ _________ ★ ____
Yana daga cikin Abinda ke Farantawa Iyali shine, Sakar mata Fuska cikin Lallausan Murmushi, Wasanni da Tsokana hadi da Barkwanci yana kara Kauna da Shakuwa tsakanin Ma'aurata Biyu,
••
Abinda baka sani ba shine, 'Yayanka da kake ganin kamar basu san komai a Fannin soyayya ba, Wallahi duk lokacin da suka ganku kaida Mahaifiyarsu cikin Walwala da Nishadi su kansu sai sunfi Sakewa dakai da yin Biyayya a Gareka, Sa6anin yadda zaka ga Wasu Mazan da ance sun koma gida shikenan yara Babu Zaman Lafiya da Sakin jiki.
••
Yallabai ka sani cewa, Murtuke fuska da rashin Walwalarka ga iyali ba shi zaisa Iyalinka suji Tsoronka ko suyi Maka Biyayya ba, Babu Abinda hakan yake Haifarwa face Kulla wutar Kiyayya ga 'Yayanka na Rashin basu Farin cikinka da Nuna kulawar Lafiyarsu ko Damuwarsu.
••
Idan baka bawa 'Yayanka Farin ciki da Annushuwa ba shin suwa zaka baiwa? Ka tuna cewa wasu suna nan suna neman Allah ya basu Iyalin Koda kuwa 'Da guda ne, amma basu samu ba, gaishi kai da Allah ya bawa kana wasa dashi.
••
Idan Muka dawo kan Mahaifiyarsu yana da kyau ace Dadadan kalamai sune suke Hadaku ba akasinsu ba, duba da wasu Mazan zaka ga Idan suka tashi fadansu ko a gaban waye yinsa suke babu Tunanin komai a Tare dasu, Wanna Tozarta kai ne, cin mutunci ne, Ai ba Haka ake ba, idan ta maka laifi kamata yayi kajata Gefe can kayi mata fada bisa Abinda ta aikata ba Daidai ba, Wallahi matukar kayi mata Nasiha cikin Salama da Kyawawan Lafuza zata Fuskanceka kuma ba zata so kara Aikata wannan Kuskure ba.
••
Ita mace tana da Matukar Rauni Uzuri a garesu da jansu a jiki shine mafi dacewa ga Namijin da ya Fuskanci wacece Mace, amma Daukar zafi da Saurin Fusata duk ba Ababen da Zasu haifar da 'Da mai ido bane, ya kamata a duba a Gyara don ALLAH.
=
=
ALLAH ka karawa Ma'aurata Hakurin Zama da juna, sannan ka Hore musu Abin da zasu farantawa Iyalansu dashi Aameen.
Mujahedeen Magaji Abubakar✍🏻
0 Comments