FA’IDODIN DA SUKE CIKIN YIN AURE:
Fa’idodin da suke cikin aure ba zasu
Kididdigu ba. Amma ga wasu ka’dan daga
ciki zamu lissafo kamar haka:-
1. Yin aure biyayya ne ga Umurnin Allah da
Manzonsa.
.
2. Yin aure yana sanya Manzon Allah (S.A.W)
farin ciki aranar lahira. Yace :
“Kuyi aure ku hayayyafa. Domin ni zanyi ma
sauran al’ummomi alfahari daku aranar
Alkiyamah”. .
3. Ta dalilin aure zaka samu wanda Zai fito
ta jikinka, har ya girma yana Kalmar
Shahada!! “LA ILAHA ILLAL LAHU
MUHAMMADUR RASULALLAHI”.
.
4. Ta dalilin aure ne zaka samu Zuriyar da
zasu yi maka addu’a bayan rasuwarka.
Wannan yana daga cikin ayyukan da ladansu
ba zai yanke ba har abada.
.
5. Yin aure ya kan zama dalilin runtsewar
idanun mutum daga kalle kallen Haramun,
sannan ya kare masa al’aurarsa daga Zina.
.
6. Ta dalilin aure ne zaka samu damar
taimaka ma ‘Yar uwarka Musulma, ka aureta,
ka Kiyayeta kenan daga Zina.
.
7. Ta dalilin aure ne zaka samu cikar
addininka, da ninkawar ladanka fiye da
wanda basu da aure.
.
8. Ta dalilin aure ne zaka samu ladan
ciyarwa da Matarka, da daukar nauyinta, da
ladan samar mata da Mazaunin da zata rayu.
.
9. Ta dalilin aure ne zaka samu damar Qara
yawan Musulman duniya ta hanyar
haihuwar da zaka samu.
.
10. Ta dalilin aure ne zaka samu damar
Karkatar da himmarka daga kan neman
biyan bukatarka ta hanyar haram izuwa ga
hanyar halal. Da kuma samun ladan saduwa
da iyalanka.
.
11. Zaka samu lada mai girma sosai idan Har
Allah ya azurtaka da ‘Ya’ya mata guda biyu,
kuma kayi hakuri dasu ka kyautata musu, ka
kyautata tarbiyyarsu, Su zasu zama
Garkuwarka daga shiga wuta.
.
12. Idan har ‘Ya’yanka guda biyu suka rasu,
kuma kayi hakuri, to Allah zai shigar dakai
Aljannah saboda wannan.
.
13. Ta dalilin aure zaka samu Qaruwar
mutuncinka da darajarka acikin al’ummah.
Ka shiga sahun mutanen da zasu iya
jagorantar lamuran rayuwar
al’ummah.
.
14. Ta dalilin aure ne zaka Samu Taimakon
Allah cikin lamarinka.
Kamar yadda Manzon Allah (s.a.w) yake
cewa: “MUTUM UKU, HAKKI NE AKAN ALLAH
YA TAIMAKESU.
1. WANDA ZAI YU AURE DON NUFIN KAME
MUTUNCINSA.
2. BAWA WANDA YAKE NEMAN ‘YANCINSA
SABODA YA SAMU DAIDAITUWA (ACIKIN
ADDINI)
3. MUJAHIDI (MAI YAKIN DAUKAKA ADDININ
ALLAH.
.
Muna tunatar da Matasan da suke da ikon
yin aure, lallai aje ayi aure, arage burin
duniya. Kullum rayuwa tafiya takeyi.
.
Ku dubi duk wadannan garabasar amma
banda Tuzurai da Gwagware, su ba zasu
samu ba..!!! Fatan mu duk masu
niyar aure Allah yayi musu jagoranci, Ya hore
musu daga falalar sa Ameen
0 Comments