AMFANIN MAN KWAKWA WAJEN RAGE TUMBI DA MAGANCE NANKARWA (STRETCH MARK).


Https://sirinrikemiji.blogspot.com/?m=1

AMFANIN MAN KWAKWA WAJEN RAGE TUMBI DA MAGANCE NANKARWA (STRETCH MARK).

A wannan satin, za mu yi bijiro da ammfanin man Kwakwa wajen warkar da wasu matsalolin da ke damun mata, wadanda suka hada da rage tumbi da warkar da nankarwa, wato ‘Stretch mark’ a Turance.
A kan samar da danyen man kwakwa ba tare da kona wani abu daga amfaninshi ba. Ba shi da wahalar hadawa, ba a bukatar yin amfani da wuta, kamar yadda na fada a baya.
 
 
Da farko, uwargida za ta samu kwakwa daidai bukata, sai ta cire bawonsa, ta yayyanka su kanana, sannan ta markade sosai. Bayan kin markade, sai ki gtace ruwan, ki dura a roba, sannan ki ajiye shi a wuri mai iska, ki bar shi ya kwana.
Da safe za ki ga mai ya taso a sama, ki sa cokali, ki yade man, ruwan ne kadai zai rage a kasa. Za ki gan shi kamar man shanu, in kuma kina bukata, kafin ki yade man, sai ki saka shi cikin firji don ya yi kankara. Hakan ya fi dadin yadewa, za ki gan shi kamar man kade. Masana sun tabbatar cewa ya fi dafaffen man kwakwan tasiri.

An nuna cewa za a iya shan shi haka nan domin rage tumbi. Baya ga wannan, za a iya amfani da shi wajen magance Amosanin kai, wato ‘Dandruff,’ don haka za a iya amfani da shi a matsayin sinadarin wanke kai (Shampoo). Ko kuma a hada shi da man kitso da man shafawa domin gyaran jiki matuka.

Ta bangaren warkar da nankarwa kuwa, babu kamar man kwawa. Da zaran kika fara amfani da shi wajen shafawa a jikinki, tabbas za ki nankarwa ta fara bacewa.

Don haka a takaice kwakwa da manta suna da matukar amfani ga mace, baicin wadannan da muka lissafa. Ruwan na magance wasu cututtukan jiki, musamman masu cututtuka a mafitsara, wanda ake kira a Turance ;Urinary infections.’
Allah ya ba mu sa’a, Allah ya taimake mu, da fatan za a wuni lafiya, kuma a rika kula da yara yadda ya kamata. Mu hadu a wani makon.

Man kwakwa ya na da amfani wajen inganta lafiyar fata, gashi, rage nauyin jiki, taimakawa wajen tace abincin jikin mutum da bayar da kariya ga wasu cututtuka da mutum ka iya kamuwa da su. Kiwon lafiya: Amfanin man kwakwa guda 7

1. Gyara fatar jiki Ana amfani da man kwakwa wajen man shafawa a jiki wanda yana da matukar fa'ida ga ma su busashshiyar fata da waskane. Man kwakwa yana kara laushin fata da yadda yake warware tamushewa irin ta tsufa a jikin fata kuma yana fa'idantuwa ga ma su ciwon kyazbi.

2. Gyaran gashi Man kwakwa yana bunkasa yalwar gashi kuma ya kawatar da shi wajen kyalli.Yana kuma bayar da kariya ta amosani da rashin karyewar gashi.

3. Ciwon Zuciya Akwai sindarin lauric acid a cikin man kwakwa wanda ya ke taimakawa wajen rage tasirin hauhawar jini da da rage daskararren maiko wadanda daman su ne ma su assasa ciwon zuciya. Yana kuma fa'idantuwa wajen al'adar mata.

4. Rage nauyin jiki Da yawan mutane su na kukan jikin su ya mu su nauyi saboda maiko da yawan teba a jikin su, man kwakwa wanda shima maiko ne amma ya na inganta narkewar duk wani daskararren maiko dake jikin mutum wajen assasasa lafiyar kayan cikin mutum. 

5. Kariya ga cututtuka Man kwakwa yana bayar da garkuwa ga lafiyar jikin mutum sanadiyar sinadarai na lauric acid, capric acid da caprylic acid. Wadannan sinadai suna inganta kariya na kananan kwayoyin cututtuka irin su kuraje, cutar sanyi da cutar HIV mai karya garkuwar jikin dan Adam. 

6. Tace amfanin abinci Akwai ma su fama da ciwon ciki wanda rashin saure tace abinci da su ka ci ke janyo musu, binciken masana kiwon lafiya ya bayyana ingancin man kwakwa wajen inganta wannan matsala ta rashin tace amfani abinci da wuri a cikin mutum.

7. Lafiyar Hakori Akwai sinadarin calcium a cikin man kwakwa wanda yake inganta karfin hakori kuma yake bayar da kariya wajen cututtuka na hakori da kara mu su haske su zama farare tar.


SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :

Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: +2348037538596
https://wa.me/message/2JY5R7B25CTJE1

JOIN US TELEGRAM GROUP: 🏷

Zamantakewar aure ga ma'aurata
https://t.me/sirrinrikemij

SHARE 🌿

Post a Comment

0 Comments