Goruba wata bishiya ce da ta dade a duniya sannan an fi samun ta ne a kasashen Afrika.
Bincike da aka gudanar akan goruba ya bayyana mamora da kuma alfanu da dama da take da shi, sakamakon sunadaran flavonoids, saponins da tananis, wanda wannan sinadaran ba sabon abu ne a wurin masana kiwon lafiya da likitoci.
ga fa’idar ta wajen magance cututtuka :
1. Masu fama da cutar asma za su iya shan garin kwallon goruba a cikin tafashashen ruwa.
2. Yana taimakawa masu samun matsala lokacin fitsari.
3. Shan garinta a ruwan dumi na taimakawa masu karancin jini a ji.
4. Goruba na maganin matsalar hawan jini.
5. Haka zalika goruba na magance cutar basir.
6. Yana kuma kare mutum daga kamuwa da cutar daji.
7. Cin goruba na kara karfin namiji.
8. Yana kuma rage kiba a jiki.
9. Cin goruba na kara karfin kashi da hakora.
10. Ruwan jikakkiyar goruba na tsiro da gashin mutum idan dai aka wanke kai da shi.
0 Comments