KO KASAN YA CUTAR HANTA WATO HEPATITIS YADDA TAKE DA ILLA?:


KO KASAN YA CUTAR HANTA WATO HEPATITIS YADDA TAKE DA ILLA?:

Da yawan mutane suna kamuwa da wannan cuta tsawon lokaci tana tare dasu ba tare da sun gane ko kuma sunji wata alama ba,kuma wannan Lalura ba karamar cuta bace domin tana iya hallaka mutum cikin kankanin lokaci.

Da farko dai Hepatitis B wani nau'in ciwon hanta ne wanda cutar hepatitis B (HBV) ke haifarwa.

 Ba kamar sauran cutukan da ake dauka wajen saduwa yake ba, wanda ake kira da Sexual transmitted disease wato(STI) wanda akan iya gane alamun su cikin kankanin lokaci,hi hepatitis b yana iya samun ka na tswon lokaci amma baka san dashi na kuma hepatitis B yana da illa domin yana haifar da kumburin hanta mai haɗari.

 Shi wanna virus na hepatitis B ana iya kamuwa dashi ta hanyar haduwar jinin mai lalurar da naka, ko ruwan jikin mutumin da ya kamu da cutar.

 Yawancin mutanen da suka kamu da cutar hepatitis B ba zasu ga wata alama ba kwata -kwata. 

 Ko da mutum ba shi da alamun cutar, kwayar cutar na iya ci gaba da lalata hanta idan ba a yi maganin ta ba.

 Wannan shine dalilin da ya sa yana da mahimmanci mutum ya rika ziyartar likita akai -akai (kamar ziyarar lafiya na shekara -shekara) don bincika alamun da yin gwaji.

ALAMOMIN DA MUTUM ZAI IYA JI IDAN YA KAMU DA WANNAN CUTA:

1. Rasin son cin abinci.
2. Yan jin kasalar jiki 
3. Yawaitar ƙananan zazzabi
4. Ciwon tsoka da gwiwa da yawan ciwon kai
5. Yawan jin tashin zuciya
6. Yawan amai
7. Fitsarin mutum yakan koma baki mai duhu.
8. Jikin mutum da idon sa ya koma kalar yello.

Wadan nan sune kadan daga Alamomi da mutum zai iya gane ya kamu da wannan cuta,da zarar ka fara jin wasu alamomi daga wadan nan kayi kokari ka tuntubi likati domin a auna ka,asan abinda ke damun ka.

Yaada za'a hada maganin wannan matsala:

1. Garin habbatussauda
2. Garin Tafarnuwa 
3. Garin habburrashad
4. Man habbatussauda.

Yadda za'a hada:

Da farko za'a samu garin habba babban chokali guda 4,garin Tafarnuwa Babba chokali daya da rabi,garin habburrashad babban chokali 3 man habbatussauda 60ml za'a hade su waje daya,sannan a kawo zuma tatacciya me kyau liter 2 a hade a ciki a juya sosai.

Za'a rika shan babban chokali 2 da safe 2 da daddare bayan anci abinci na tsawon wata 2 insha Allah zaa samu waraka,bayan an gama sha aje asibiti ahi gwaji.
Allah yasa mu dace.

Rubutawa tare da dorawa daga zauren maijalalaini.com 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :

https://wa.me/message/2JY5R7B25CTJE1

Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: +2348037538596
Follow this link to view our catalog on WhatsApp: https://wa.me/c/2348066627317

JOIN US TELEGRAM GROUP: 🏷

Zamantakewar aure ga ma'aurata
https://t.me/sirrinrikemij

SHARE 🌿

Post a Comment

0 Comments