Kada Ka Furta Wadannan Kalaman A Gaban Mace A Farkon Haduwarku:


Kada Ka Furta Wadannan Kalaman A Gaban Mace A Farkon Haduwarku:

#Tsangayarmalamtonga 
SHARE 🔮

Na kanga wasu mazan suna kuskuren furta wasu kalamai marasa daraja a farkon haduwarsu.

To a gaskiya kada ka sake ka rika furta irin wadannan kalaman domin zasu hanaka samun soyayyar wacce ka furtawa su.
Wadannan kalaman sune:

 
Tabbas ana iya shawo kan mace idan musu ya hadaku. Amma hakan na iya faruwa ne ba tare da kayi musun da ita bane domin neman soyayyar ta.

Idan Ka ja macen da kukayi haduwar farko kuma kake sonta da musu kana iya rasa soyayyar ta.

Duk wata mace Gimbiya ce, bita ta yadda take so cikin sauki zaka samu kanta.

 Amma da zaran ka mata musu zata daukeka a namiji mai tsaurin hali hakan zai sa ta gujeka.

2: Kada ka sake ka aibata wani abu da ka gani a tare da ita koda kuwa shigar data yi ne. Kana hakan kuwa ka rasa ta.

Akwai mazan da suke nunawa mata iyaye da nuna musu shigar da suka yi ko kwalliyar su bai dace dasu ba a haduwarsu na farko. Kada kayi hakan.

3: Wasu mazan tsabar zakewa yana haduwa da mace a farko zai yi kokarin kai mata hannu ya taba mata jiki. Abokina mace ko cinikin jikinta take wasu na da zabi. Bere kuma bakasan ko wacce iri bace har ka kai mata cafka a haduwarku na farko. Kuskure ne.

4: Mata sunada tsarguwa. Kada Ka sake kayi rada a gaban mace da kuka soma haduwa. Domin kawai zata dauka kayi mugun magana ne a kanta kamin kuma ka shawo kanta zai dau lokaci.

5: Kada ka kuskura aibata mata ko kushe wata a gaban macen da kukayi haduwar farko. Hakan zai sa ta samu shakku akan ka.
 
Da fatan maza musamman gayu da suke tunanin sun hadu zasu fahimta.

Post a Comment

0 Comments