Illar Ajinomoto ( Kafi Zabo )


Illar Ajinomoto ( Kafi Zabo ) Harisu Sani Hayatu Sharada 

Illar farin maggi ga rayuwar dan adam. Kamata yai ace duk fadin duniya bana nan gida Najeriya ba a daina amfani da farin magi.Tabbas bincike ya nuna farin magi ko kafi zabo wanda ake kira a turance (monosodium glutamate) yana da matukar illa ga dan adam, babban illarsa kamar haka:

Yana rage karfin namiji. ta hanyar kashe sinadarin dan adam. Sannan babbar illa ta biyu shine Yana rage kaifin kwakwalwa. Saboda haka kamata kwata-kwata muguje shi, mu daina ammani dashi. Saboda haka akwai nau'uka na magi masu dama dama kamarsu maggi dunkule, Rayco da sauransu, inaga zai kyau ace su ake amfani dasu, suma Kada a cika sawa da yawa. daddawa ta gargajiya da ake ki' "itace kan gaba a wajen Amfani Da sa lafiya. 

An hana amfani da maggin Ajinomoto a kasar Pakistan - a Ranar 3 Ga watan Maris 2018. Babban alkalin Pakistan Mai shari'a Mian Saqib Nisar ya haramta sayar da gishiri Ajinomoto na kasar Sin, lura da cewa yana da hadari ga lafiya.
Babban alkalin kotun ya ce ba za su yarda a sayar da gishirin ba. 

A ranar 15 ga Janairu, Hukumar Abinci ta Punjab (PFA) ta haramta Ajinomoto bayan da hukumar ta gano yana da hadari ga lafiya.

A cewar PFA, gishirin ya ƙunshi Monosodium glutamate (MSG), mai ƙara dandano da aka ce yana haifar da asma, ciwon kai, har ma da lalacewar kwakwalwa.

A cewar wasu rahotanni, yin amfani da wannan sinadari na yau da kullum na iya haifar da al'amura na dogon lokaci kamar hawan jini, Autism, rashin daidaituwa na hormonal, farfadiya, rashin lafiyar abinci, ciwon asma, ciwon daji na mahaifar mata.

Masana sun tabbatar da cewar maggin yana da babbar ila ga kwakwalwar mutum - An haramta yin amfani da maggin a kasashe da dama ciki kuwa harda kasar Amurka.

Kasashe kamar China da Japan sun haramta amfani da ajinomoto a cikin kayan abinci.

An sanya dokar ta hana amfani Ajinomoto a cikin abincin jarirai da basu wuce wata 3 ba a kasar turai, da kuma rage yawan sanya shi a abinci a wasu kasashe 50.

Post a Comment

0 Comments