DON ALLAH MATASAN AREWA KU FAHIMCI WANNAN.


DON ALLAH MATASAN AREWA KU FAHIMCI WANNAN. 

Nasir I. Mahuta

Shin ko kun lura cewa matasan Inyamurai da Yarabawa sun fi matasan Hausawa zama attajirai da iya dogaro da kansu? Shin ko ka san dalilin da ya sa hakan ke faruwa? Biyo ni cikin wannan rubutun.

Matasanmu na Arewa suna da jajircewa da kuma kokarin neman na kansu bakin gwargwado, idan ana batun kokarin neman na kai ne ma za'a iya cewa matasan Arewa ba su da tamka. Amma idan ana batun nasara to ba'a kallon kokari kadai, ana kallon sakamakon da kokarin ke bayarwa.

1. Matasan Arewacin Nigeria za ka ga sun fi kwarewa wajen neman hanyoyin samun kudi ta hanyar leburanci maimakon kasuwanci. Ko da matashi ya bar garin su da niyar zuwa wani garin neman kudi, idan ya je garin za ka ga abinda zai yi shi ne leburanci maimakon kasuwanci. Mai ke kawo haka?

Hanzari da gaggawar samun kudi shi ke tunzura matasanmu yin leburanci, domin leburanci ne kadai za ka fara yau kuma ka fara samun kudi yau, sabanin kasuwancin da sai ka yi yaron gida na tsawon shekaru kafin kila ka fara samun kudi. Saboda matashi na son samun kudi da gaggawa sai ya zama Dan Achaba, Dan Dako, Magini, Dan Kwadago, Dan Kabu-Kabu da dai sauransu.

Tabbas a tashin farko kare na iya wuce mota, ma'ana matashin da ke leburanci yana iya fin matashin da ke koyon kasuwanci samun kudi a matakin farko, amma a karshe za ka ga mai leburanci shi ne ke cikin talauci shi kuma mai koyon kasuwanci ya zama attajiri. Shi ya sa a duk inda ka ga matasanmu a Kudancin Nigeria za ka ga su ke rayuwar kaskanci da talauci, idan kuma ka ga matashin Inyamuri koda a Arewacin Nigeria ne za ka ga shi ke rayuwar jin dadi.

2. Matashin Inyamuri tun farko zai fara neman wanda zai yi masa yaron gida ne, wani lokacinma iyaye ne da kansu su ke daukar yaro su kai wa wani Dan kasuwa kuma har su biya shi da niyyar yaron ya yi masa bauta a matsayin yaron gida. Yaron zai kwashe a kalla shekera 5 yana yi wa mai gidansa hidima shi kuma yana koyon kasuwanci. A dalilin zamansa da mai gidansa mutane za su san shi, customers za su saba da shi, zai san sirrin kasuwancin, zai koyi yadda ake tattalin kasuwanci, zai koyi yadda ake habbaka kasuwanci. Bayan shekara 5 sai a sallame shi da kudin da bai wuce leburan matashin Arewa ya same su a wata biyar ba. Amma da ya ke yaron ya samu experience na kasuwanci, bayan shekara daya kacal sai ka ga shi ma ya zama abin kwatance, shi ma sai ya dauko wani yaron ya koya masa kamar yadda aka koyar da shi. A hankali sai ka ga experience na kasuwancin yana yawo a tsakanin matasansu.

MAGANAR GASKIYA

Maganar gaskiya matasanmu su cire Mentality na yin leburanci a ransu, duk rintsi ka yi kokarin koyon kasuwanci ko kuma sana'a, kada ka yarda ka jefa kanka a leburanci domin leburanci zai kashe maka zuciya kuma ya kashe maka lokaci sannan ya kashe maka lafiyar jiki. Idan har za ka iya jure yin shekera 6 a primary, shekera 6 a Secondary mai zai hana ka jure shekera 3 ko 5 kana koyon kasuwanci  

Shekarun da za ka jure su ne wanda za su chanja rayuwarka daga talauci zuwa arziki, idan za ka cinye shekarun kana leburanci karshe dai za ka ga talaucewa kawai ka ke yi.

Wasu za ka ga sai sun fara koyan kasuwanci kamar abun arziki sai abokansu su rinjaye su daga nan su daina zuwa su koma achaba. Domin yana kallon abokinsa da ke yin Achaba yana facaka da kudi shi kuma mai gidansa ba ya sakar masa kudi kawai sai ya daina zuwa ya yi zuciya. Ya rage gare ka, ka yi leburanci don ka dinga samun kudin kashewa, ko kuma ka tsaya ka koyi kasuwanci don ka zama attajiri.

Post a Comment

0 Comments