AMFANIN GANYEN DODDOYA ( Scent leaf ) GA LAFIYAR DAN ADAM.


AMFANIN GANYEN DODDOYA ( Scent leaf ) GA LAFIYAR DAN ADAM. 

Ganyen ƙamshi ( Ocimum gratissimum ) ganye ne na ƙamshi wanda asalinsa Dan yammacin Afirka Ne amma ya yadu zuwa Indiya da kudu maso gabashin Asiya. 

Yana girma har zuwa 1-3 m A tsaye tare da rassa da yawa suna tasowa daga tushe. 

Ganyen kamshin na iya samar da bitamin, antioxidants, da ma'adanai. Abun cikinsa na mahimmani na iya ba da wasu fa'idodin magani.

Ga Wasu daga cikin muhimman abubuwan gina jiki da ke tattare da Shi Da Su ka hada da:

1, fiber
2, Protein
3, Vitamin A 
4, Vitamin B
5, Calcium
6, Vitamin K
7, Potassium 
8, Magnesium
9, Iron
10, Zinc
11, Phosphorus

AMFANIN GANYEN 'DADDOYA🌿 WATO GANYEN RAIHAN KO KUMA A TURANCE (SCENT LEAVES)🌿 DA YADDA AKE SARRAFA SHI🍵 

(1) Yana narkan da abinci 
(2) Yana tsare mutum daga kamuwa da ciwon zuciya💓
(3) Yana rage tasirin Ciwon suga (diabetes)
(4) Yana rage radadin ciwo 
(5) Yana kashe bacteria da germs(kwayoyin cuta)
(6) Yana rage nikotin(nicotine)
(7) Yana tasirin wajen sanyi mai kama Gabobi 
(8) Yana Amafani wajen mace mai Neman haihuwa Yana wanke mahaifa(boost fertility)
(9) Yana maganin sauro (fight mosquito)
(10) Yana taimakawa wajen mura da tari 

YADDA AKE SARRAFA GANYEN DADDOYA🌿

(1) Yadda ake amfani da Doddoya wajen narkar da abinci ana hadata da lemon grass adafa ariqa sha.

(2) Yadda ake Amfani da dodoya wajen magance kamuwa da ciwon zuciya zai arika dafata da danyen citta Ana sha kaman tea 

(3) Yadda aka amfani da dodoya wajen ciwon suga diabetes Asami ganyen garahuni sai A hada su A dafa Arikasha Kofi daya da safe kafin aci abinci Kofi daya da yamma har sati 3.

(4) Yadda ake amfani da dodoya wajen rage radadin ciwo Asami garin kanunfari Rabin cokali ahada da ganyen dodoya adafa arika sha.

(5) Yadda ake amfani da dodoya wajen riga kafi kamuwa da cutar bacteria za A same shi A sai arika sawa cikin abinci ana dafawa.

(6) Yadda ake amfani daita wajen rage nicotine wannan yafi amfani ga mai shan taba ko mai cin goro ' 
ajajjagashi ko ayi blending dinshi tare da citta danye guda daya da bayan an gama sai azuba zuma a ciki asha.

(7) Yadda ake amfani da doddoya wajen sanyi mai kama gabobi za'a sami doddoya da citta danye da lemun tsami da tafarnuwa da saiwar sanya sai adafa arinka sha

(8) Yadda ake amfani dashi wajen mace mai Neman haihuwa Yana wanke dattin mahaifa zata sami dodoya da ganyen magarya ta dafa a Rinka kasha " kuma anaso duk abincin da zata dafa ta tabbatar da tasa ganyen dodoya a ciki.

(9) Yadda ake amfani da dodoya wajen maganin sauro idan akayi hayaqinta yana Koran sauro 
(10)Yadda ake amfani da dodoya wajen maganin mura ana samun ganyen dodoya da citta danye sai adafa ariqa zuba Zuma anasha.

Post a Comment

0 Comments