Abu guda 6 na sunnar Annabi (SAW) wadanda ya kamata kowadanne iyaye su yiwa jaririn su bayan haifar sa:


Abu guda 6 na sunnar Annabi (SAW) wadanda ya kamata kowadanne iyaye su yiwa jaririn su bayan haifar sa:

Aliyu Aminu Fasihi


Abu guda 6 na sunnar Annabi SAW wadanda ya kamata kowadanne iyaye su yiwa jaririn su bayan haifar sa.

AIKA ZUWA SHAFUKAN SADARWA SHARE 

Abubuwan da ke ciki :

1. Huduba (Kiran sallah ta radin suna a kunnen jariri)
2. Duren dabino
3. Radin suna 
4. Yankan hakika ( Kafin ko ranar bakwai 7 )
5. Aske kan jariri ko jaririya 
6 . Kaciya


 Bayan an haifi jariri wadannan sune ayyukan da sunnah ta koyar da ayi wa jariri. 

Gidauniyar musulunci ta The Islamic Information, itace ta kawo wadannan mahimman ayyuka na sunna, mu kuma daga nan Labarun Hausa, zamu ruwaito muku su kamar haka:

 
1. Huduba (Kiran sallah ta radin suna a kunnen jariri)

Idan aka haifi jariri, abu na farko da ake fara yi masa shine kiran sallah na radin suna, a kunnen dama, sannan sai a karanta ikama, a kunnen sa na hagu. 

jariri

Abu guda 6 na sunnar Annabi SAW wadanda ya kamata kowadanne iyaye su yiwa jaririn su bayan haifar sa
Wannan yazo a cikin hadisin Tirmizhi, hadisi mai lamba 1514, Inda aka ruwaito cewa manzon Allah SAW din yayi haka. 

An ruwaito daga Ubaidullah Bin Abi Rafi : cewa baban sa yace :


” Naga manzon Allah SAW ya yi kiran sallah a kunnen Al-hassan Bn Ali, a lokacin da nana Fadhima ta haife shi, kiran sallah “.

Tirmizhi 1514.
 

2. Duren dabino

Yana daga sunnah, idan an haifi jariri, a tauna dabino a sanya masa ruwan a bakin sa yadda zai iya hadiyewa. Idan ba’a sami dabino ba, za’a iya sanya wa jariri Zuma a bakin sa. Ana son ace dattijo ne yayi hakan, ko kuma wani malami. 

Aikata wannan sunnah yana kare jariri daga zama dakiki. Binciken kimiyya ma ya tabbatar da haka. 

Nana Aisha, Allah ya kara mata yarda, ta ruwaito cewa,

“mutane suna kawo jariran su sabuwar haihuwa, gurin manzon Allah SAW domin ya sanya musu albarka, kuma ya yi musu duren dabino ( Attahnik )”

hadisin sahih Muslim mai lamba ta 2147.

3. Radin suna 

Kyakkyawan suna yana da matukar mahimmanci a musulunci. Manzon Allah SAW ya zabawa jarirai kyawawan sunaye. Zaku iya sanya wa jariran ku, sunaye irin na magabatan sahabban manzon Allah SAW. A wasu al’adun, ana radawa jariri suna ne a ranar da za’a yi masa yanka, ranar bakwai kenan da haihuwar sa. 


4. Yankan hakika ( Kafin ko ranar bakwai 7 )

A Takaitacciyar ma’ana, hakika tana nufin sadaka da ake yiwa jariri, domin neman kariya ga jaririn ka daga duk wani abin ki. 


” Mazon Allah SAW, ya yanka rago daidai ga Hassan da Hussaini, RA

Hadisin Abin Dawud 2834.
Idan namiji ne a yanka guda biyu, idan da hali, idan kuma mace ce a yanka guda daya. 

Buraida RA, yace 

” A lokacin jahiliyya, idan dayan mu ya sami karuwa, sai mu yanka tunkiya, mu shafa jinin a kan jaririn. Bayan Allah ya azurta mu da musulunci, sai muke yanka tunkiya, sannan mu aske kan jaririn”.

Abu Dawud 2836. 

5. Aske kan jariri ko jaririya 

Wajibi ne, a aske kan jariri na miji ne ko mace, a ranar 7 ga haihuwar sa ko haihuwar ta, tare da yi masu yanka, duk da shi yanka mustahabbi ne. 

An ruwaito cewa, Muhammad Bn Ali Bn Hussain, ya ruwaito cewa, 

Ali Bn Abi Dalib, yace :

” Manzon Allah SAW ya yi wa, Alhassàn yankan hakika da wata tunkiya, sannan sai yace, Ya ke Fadhima, ki aske masa kan sa, sannan ki auna nauyin gashin da kimar azurfa, ki bayar da sadaka, ” sai yace, sai na auna shi, ya na da kimar Durham ko wani yanki na Durham.”

 Hadisin Tirmizhi 1519.

6 . Kaciya

Ana yi wa yaro Kaciya ne kafin isa girman sa, a shawarce ma kamata yayi a yiwa jariri Kaciya a ranar sunan sa. Manzon Allah SAW ya yi wa sayyadina, Hassan da Hussain Kaciya a ranar sunan su.

Allah ya bamu ikon kula da tarbiyyar yayan mu, ya sanya musu albarka.

Post a Comment

0 Comments