Wasu Abubuwan Da Suke Iya Kashe Aure Cikin Sauki:


Wasu Abubuwan Da Suke Iya Kashe Aure Cikin Sauki:

SHARE 💕
#TsangayarMalam 

Da akwai abubuwa da dama da suke kashe aure, sai dai wadannan da zamu kawosu a wannan darasin sun fi saurin kisan aure. Ga abubuwan nan kamar haka:
 
1: Rashin Sauke Hakkin: Wannan matsalace babba dake saurin kashe Aure.
Dukkanin ma'aurata ya kamata susan hakkin daya rataya a wuyansu kamin suma yi auren. Domin dukkanin su miji da mata ko wannen akwai hakki guda akansa. A yayin da guda ya kasa kula da wannan hakin dake wuyansa nan take aure yana iya mutuwa.

2: Rashin Sadarwa Mai Inganci: A irin wannan yanayin karamar magana guda zai yiwa guda sai kawai ayi masa mummunar fassaran da zai iya jawo matsalar da saki na iya shiga.
Yanada da kyau ma'aurata ya zama suna da kyankyawan sadarwa na fahimta a tsakaninsu. Yadda duk abunda guda bai fahimta ba yana da daman neman Karin bayani.

#shawarane
 
3: Kwatanta Juna Da Wasu: Ana samun macen da zata rika ganin kasawar mijinta har zata rika masa misali da tsohon mijinta idan ta taba aure ko kuma wasu makotansu idan suna da su.
Hakan nan suma mazan sunada wannan halin da nunawa matansu wata can ta fita da wani abun.

Irin Wadannan kwatance na hasala duk wanda aka yiwa, da zai iya furta kalama mara dadin da zai iya jawo saki.
Bai kamata ba ma'aurata su rika kwatanta zaman aurensu da wasu mutane can ba. 

4: Yawan Shigo Da 'Yan Uwa Da Abokai: Muddin ma'aurata bazasu iya dai-dai ta kansu ba a lokutan da suka samu rashin fahimta ko sabani har sai sun shigo da 'yan uwa ko abokai cikin maganar, tabbas wannan aure bazai yi tsawon rai ba.

Ba duk 'yan uwa bane suke iya baiwa nasu hakuri a lokacinda aka cutar dashi a zaman aureba. Musamman idan ana yawan samun matsalar da ake shigowa dasu. Haka suma abokai basu cika bada shawara na kwarai ba idan har sun fahimci a zaman auren ana musgunawa nasu.

Don haka ma'aurata su koyi iya sulhuta kansu da kansu, ta hakan ne kawai zasu baiwa aurensu damar yin tsawon rai. 

5: Zargi: Wanda shine abu na farko kuma babba dake saurin kashe aure.
Zargi ke sa mace ta rika bincikar wayar mijinta haka shima mijin. Zargi ke sa wasu ma'aurata suke bibiyan junansu domin gano abunda suke yi.

Na sha bada shawaran cewa, duk kankantar zargi idan kana dashi akan wacce zaka aura, hakura da auren shi yafi maka alheri.

Akwai mazan da suke amfani da asiri domin kama matansu idan suna zarginsu. A fahimtana duk wannan shirme ne kuma wauta ne ka yayatawa duniya abun bakin cikin da matarka take yi. Musamman ma ace kun haihu da ita. Maimakon hakan ka saketa kawai zai fi maka kwanciyar hankali da wannan muzantawan.

Akwai matan da suke zuwa suyi dambe da 'yan matan mazajensu. Wasu ma otel ko akan titi suke wannan rashin mutuncin. Kin gama tonawa kanki asiri wai nan da sunan kishi ko zargi.

Kamata yayi ki nemi saki kawai saboda korafin da kike da shi akansa na Zina, amma ba sai kinje kinata kokuwa da wata macen da ba laifin ta bane idan mijinki na zuwa wajenta.

Idan ma'aurata zasu kiyaye wadannan abubuwan. Da taimakon Allah zasu zamu Zamantakewar aure mai inganci.
Allah Ya sa mu dace.

Post a Comment

0 Comments