Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban amsar tambaya a kan siffofin mace ta gari. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su:
Siffa ta biyu da ke kammala nagarta ’ya mace ita ce:
Da’a: Ma’anarta tana da fadi da kuma girma, tana nufin kankan da kai, yin ladabi da biyayya, saduda, neman kusanci, so da kauna, kyautata zato, tsarkake tunani, nuna so da kauna, yin kaffakaffa wajen zartar da al’amura, kiyaye dokoki, aiki da hankali wajen mu’amala, sadaukarwa, tausasawa, kiyaye kalami, kunya, girmamawa, yarda amincewa, darajawa da sauran kyawawan halaye.
Kuma duk wadannan a yi su cikin aminci da dadin rai da sakankancewa ba tare da tursasawa ba, wato a rika yi a kan dole alhali zuciya ba ta so kuma ba ta aminta ba. A takaice dai da’a ita ce nagarta da tsarewa a aikace!
Da’ar ’ya mace mafi girma ita ce ga Mahaliccinta Allah Madaukakin Sarki, sannan ga mijinta, sannan ga iyayenta sannan ga dukkan wuraren da ya kamata ta nuna da’a.
Tsarewa na nufin tsare dokoki da umarnin Allah a koyaushe duk a ciki da wajen aure da kuma na addini da rayuwa gaba daya. Babban abin tsarewa ga mace dai shi ne mutuncinta.
Allah Ya haramta mata bayyana adonta ga duk wani namiji da ba muharrami ba da kuma tsare amanar kanta da amanar gidan mijinta da ’ya’yan mijinta.
Wadannan sinadarai biyu da’a da tsarewa su ne tubulin ginin nagarta da kamalar ’ya mace, in ba daya daga cikinsu, to babu kamala kuma ba nagarta. Wadannan siffofi guda uku su ne ginshikin nagartar ’ya mace.
Duk ’ya macen da ba ta da wadannan abubuwa uku ko kuma sun yi karancin ainun to akwai alamar tambaya a cikin nagarta da kamalarta. Wani bangaren kuma na nagartar ’ya mace shi ne macen da ta jiku da macentaka a cikin kowane yanayi nata, ta yadda zama da tafiya da magana da rubutu da sauransu za ta yi su tare da sa hila da fi’ iliyya irin ta ’ya mace, ta yadda ko yaro take face wa majina, in mijinta na kallo sai hakan ya dauke masa hankali saboda yadda dabi’ u da yanayin ayyukanta suke cike da hilar macentaka.
Domin Manzon Allah (SAW) ya ce mafi dadin more rayuwar duniya shi ne samun matar auren da kallon ta yake kayatarwa.
Kayatarwa ba wai ana nufin ka rudu da kyan siffar jikinta kadai ko iya kwalliyarta ya dimautar da kai kadai ba, ana kuma nufin kallon ta yana saukar maka da natsuwar cewa ka auri cikakkar mace, mai natsuwa, mai kyan hali, mai ladabi da biyayya, mai tsoron Allah, wacce ka san tabbas ba za ta wulakanta ka ba kuma ba za ta ci amanarka ba.
Kuma ana nufin macen da ta cika ta tumbatsa da hila da fi’iliyyar macetaka ta yadda ko wanke-wanke take yi sai mijinta ya shagaltu da kallon ta, to ina kuma cewa ta juyo hankalinta gare shi tana zuba masa madarar so da kauna? To yaya ake gane mace mai kunshe da wadannan siffofi?
To gaskiya wadanda sukan san macen suka cudanya da ita ce kadai za su iya sanin wannan dabi’un game da ita.
Shi ya sa yake da matukar alfanu ga manemin aure ya zurfafa da kyautatawa da kuma yin hakuri wajen bincike har sai ya gamsu da halaye da dabi’un wacce zai aure don guje wa auren asara da karya tattalin arzikin.
Don yawan mutuwar aure illarsa ba ga su ma’auratan ba ne kadai, yawan mutuwar aure na komar da al’umma baya da karya tattalin arzikin kasa, babbar illarsa kuwa ita ce yara su tashi ba lullubi da rahamar uwa da uba a tare da su.
Matasa da sauran manema aure sai kun dage da yin juriya in kuna son dacewa da irin wannan mace tagari ku juya baya ga kyalkyal banza, domin a wannan zamanin, saboda tasiri na kallon fina-finai, ga mata nan jingim sun kware wajen yatsina da rangwada da karairaya ta yadda nan da nan za su dulmiyar da mai raunin ruhi, amma kuma ba tarbiyya, ba dabi’u nagari, sannan wasu ga kwalliya ga tarbiyya amma ba rangwada da hila.
Wasu kuma ga hankali da addini amma ba kwalliya da rangwada, don haka yana da kyau yin dogon nazari wajen neman matar aure.
Sai mako na gaba insha Allah. Da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin. (MAIMAITAWA).
0 Comments