Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani:

Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani:


Shin ko kasan cewa cikin mutum na aiki ne kamar injin markade? To haka batun yake, wasu lokutan mutane kanci abubuwan da suke da wahalar narkewa a ciki, amma da taimakon lemon Cittar da aka hada shi da lemon tsami da dan gishiri asha kafin ko bayan cin abinci, kan taimaka sosai wajen saukaka narkewar abincin da muka ci.

Idan kowa aka sha kafin cin abincin to zai kara sanya Mutum yaci sosai, saboda lemon yana farfadoda sha’awar cin abinci cikin lokaci kalilan.


1⃣ Maganin Mura


Hausawa suka ce a rashin sani yasa Kaza ta kwana kan dami. Idan kai ko wani yana korafin majina ta dame shi a kirji ko baya iya numfashi yadda ya kamata ko kuma cikinsa ya cushe kamar ana cunkoson ababen hawa, maza bashi wanann shawarar , ya samu ya hada lemon Citta ya dan sanya Attaruhu da zuma ya sha shi da zafinsa a kalla sau biyu ko uku a rana. Ko lemonta ita kadai aka sha zai yi maganin dashewar murya.

2⃣ Maganin gajiya da ciwon jiki


A kwanan baya ta kawo muku rahoton yadda shan Paracetamol da Ibuprofen da Mata masu ciki keyi, na iya hana zuri'arsu haihuwa nan gaba, a yanzu ga hanya sahihiya don gujewa shan kwayoyin da zasu iya illata lafiya.

Shan lemon sabuwar danyar Citta zai taimaka mutuka gaya wajen kawar da gajiya da kuma ciwon jiki domin Cittar na dauke da sinadaran dake karawa garkuwar jiki karfi.

Domin magannin ciwon baya kuwa, sai a samu lemon Citta (Juice) cikin babban cokali a hada tare da Man Zaitun a zuba wurin a rika yiwa Mutum tausa ana murzawa, dazar an farka da safe za’a nemi ciwon a rasa.

Idan kuma ciwon hakori ne, sai a sanya sabuwar danyar cittar karama a tsakanin hakori da dadashin zuwa wani lokaci. Haka zalika idan ciwon kai.

Post a Comment

0 Comments