Kuskure Ne Yiwa Mace Wadannan Abubuwan:


Kuskure Ne Yiwa Mace Wadannan Abubuwan:

SHARE 💕
#TsangayarMalam 

Akwai wasu dabi'u da hakaye na wasu mazan da suke cutar da mata dasu. Wasu mazan kuwa suke zubarwa kansu mutunci dasu. Akwai mazan da suke rasa soyayyar da ake musu saboda su.
Duk namijin da yake son yayi kyankyawan mu'amala da mace musamman wace yake nema da aure ko wacce ya aura. To ka guji yiwa mata wadannan abubuwan kamar haka:

 
1: Kada Ka Furtawa Mace Kalmar So Bada gaske kake ba.

2: Duk Munin Mace Kada Kace Mata Mummunace Ita.

3: Kada Ka Sake Ka Kwatanta Mace Da Wata Muddin Ba Cewa Zakayi Ta Fita Da Wani Abun Ba.

4: Kada Ka Dakawa Mace Tsawa.

5: Kada Ka Sake Ka Tona Wani Sirrin Da Mace Ta Baka Ko Ta Fadamaka.

6: Kada Ka Yiwa Mace Alkawarin Da Bazaka Cika Ba.

7: Kada Ka Ci Amanarta Musamman Da Wata Na Kusa Da Ita.

8: Kada Ka Gwaleta A Cikin Mutane Ko Mata Gyara Na Kaskanci.

9: Kada Cutar Da Ita Saboda Soyayyar Datake Maka.

10: Kada Ka Zama Mai Tsautsauran Ra'ayi Ko Akida Akanta.


Mace idan tana yinka, tana yinka ne gaba dayanta jini da tsoka. Ranta da mutuwa. Don haka amfani da wannan nakasar kada ya baka damar ka cutar da ita. 

Kada ka sake kayiwa macen da take sonka abunda bazaka so ayiwa ta kusa da kai ba.
Mata Mutanen Mu.

Post a Comment

0 Comments