Yadda Zaki Nunawa Saurayinki Na Nesa Kina Tare Dashi:


Yadda Zaki Nunawa Saurayinki Na Nesa Kina Tare Dashi:

SHARE 💕
#tsangayamalamtonga 

Soyayyar nesa, soyayya ne da yayi tasiri a wannan lokacin da ake da hanyoyin sada zumunta ta internet da dama.

Masoya sukan kamu da soyayya junansu ba tare da sun ga junansu a zahiri ba kuma ina iya kasancewa ba a garin daya suke ba.

Sai dai saboda rashin sanin yadda zasu tarairayi juna duk saboda nisan da suka yiwa juna.

Mata, ga wasu hanyoyin da zaku nunawa masoyanku na nesa domin tabbatar musu da cewa kuna sonsu.

 
1: Yawan Kiransa: Idan kina son tambatarwa saurayinki na nesa kina tare da shi, ki yawaita kiransa ta waya kina jin lafiyarsa. 

Idan zaki iya kiransa da safe kamin ya fita nema. Da rana kamin ya tashi daga wajen aiki ko sana'a da kuma dare kamin ya kwanta, babu shakka zaki mamaye zuciyarsa. 

2: Hada Shi Da Wani Na Kusa Dake: Idan garin da yake kina da wani na kusa dake namiji, yi kokarin hadasu su ga junansu. Hakan zai tabbatar masa da cewa kina tare dashi. 

Idan kasar da yake ko garin da yake baki da naki da hakan zai yiwu. To kiyi kokarin hadashi da akalla mutane biyu nake su gaisa da shi tare da nuna masa yadda kike kaunarsa da kuma su masa kashedin gudun yaudara.
 Kina yiwa namijin da kuke soyayyar nesa da shi zai tabbatar da kina tare dashi.

3: Kiransa Ta Bidiyo: Ki samu lokaci kina kiransa ta bidiyo (video call) a lokaci da musamman.

Irin ranakun Sallah, ko duk ranar Jumma'a ya zama kuna yin irin wannan biyon koda na mintuna 10 ne domin ganin fuskokin juna har da na kusa da ku.
Kiran bidiyo kirane da yake karfafa soyayya ga masoya.

4: Tura Masa Kalamai Na Soyayya: Ta hanyar amfani da Whatsapp dinki ko shafukanki na sada zumunta domin turawa masoyinki na nesa kalamai masu dadi na soyaya. 
Akwai katunan soyayya da ake samunsu ta internet, kina iya daukosu ki gyaraso daidai da kalaman da kike so harma da sunan ki dana masoyinki kina iya sawa.
Duk wannan hanyace da zai karfafawa namiji mai sonki soyayyar da yake miki. 

5: Amfani Da Social Media Ki: Kiyi amfani da duk social media da kike dasu domin nunawa duniya kin kamu da soyayyar wani yadda zai iya gani yaji dadi.

Duk da wasu matan na gudun shelanta masoyansu ta hanyar saka hotunansu ko ambatan sunansu. Hakan bazai hanaki yin inkiyar da muddin ya karanta yasan da shi kike yi.

 
Zamu ci gaba...........

Post a Comment

0 Comments