Wasu Abubuwa 10 Da Bai Dace Matan Aure Suna Yi Ba:
SHARE 💕
#Tsangayarmalamtonga
Wasu matan auren sun maida aikita wasu abubuwa tamkar ibada saboda yadda suka ga akasarin mata suna yi.
Ga wasu abubuwan da matan aure suke aikatawa daya kamata su daina.
1:Fifita 'Yan Uwa Da Abokai Akan Mijinki: Akwai matan da idan suna tare da 'yan uwansu ko kawayensu basu da lokacin sauraren mazansu.
Wannan babban kuskure ne. Muddin kika zama mace mai irin haka zaki jawowa mijinki raini da kaskanci wajen wadanda kike raina shi a gabansu.
2: Rashin Yiwa Miji Fara'a: Akwai matan da idan anga suna Fara'a to bada mijinsu suke yi ba.
Irin wadannan matan babu raha a tare dasu bare yiwa miji barkonci. Kullum fuskansu a murtuke.
Wajen hira basu da lafazi mai kyau da zasu furtawa miji. Wadannan mata basu da wani abunda suke debewa miji kewa dashi sam.
Hakan bai dace ba ga duk wata matar aure da kuma take son ta zauna da mijinta lafiya.
3: Kin Yarda Da Miji: Akwai matan da basa yarda da mazansu kwatakwata sai anyi tashi hankali. Akwai kuma matan da sai idan sune suke so sannan miji zai sadu dasu. Kana akwai matan da suke cewa sai miji ya biyasu wasu kudi kamin yayi Jima'i da ita. Har ila yau akwai matan da suke baiwa mazansu damar tabasu da sharadin wani abun da mazan suka cika ko zasu cika.
Duk macen da take yiwa mijinta daya daga wadannan abubuwan ba macen arziki bace. Irin wadannan matan suke jefa mazansu shiga zina da wasu matan idan basu da hali ko Izinin kara aure. Ko kuma idan suna da izzinin dole suke kara aure ba domin suna ra'ayin hakan ba.
Wadannan dabi'un ba na matan kwarai bane. Kada mace ta maida gabanta ya zama wani tarko ga mijinta.
4: Yin Wasu Abubuwa Babu Neman Shawara Ko Izzinin Miji: Akwai matan da idan sun tashi yin wani abu nasu babu ruwansu da neman neman Izinin miji bare ma su nemi shawaransa.
Irin wadannan matan sai sun yi abunda ya dawo matsala sannan ma mazansu suke sani. Akwai wasu matan sai sun mutu mazansu suke samun labarin suna da gidajen haya guda kaza ko motocin haya guda kaza idan 'yan uwanta da wadanda ta baiwa abun suka kasa samu daidaituwa yadda zasu cinye dukiyar sannan mijin zai ji a dole.
Wannan ba dabi'a bace ta matar arziki ba. Akwai abunda dole kina neman izzinin miji kamin kiyi shi, akwai kuma wanda kike neman shawaransa. Don haka kada ki biyewa son rai idan har da gaske kike yi na neman gamawa lafiya.
5: Daurawa Miji Abunda Bazai Iya Ba: Akwai matan da suke daurawa mazansu hidimar abunda yafi karfinsu kuma su nace suce dole sai anyi musu.
Irin wadannan matan idan mazan suka biye musu kuma basu da karfin yin hakan, wannan ke sasu sace sace a inda suke aiki. Ko salwaltan da jarinsu idan masu karamin karfin nesu. Ko kuma kaskantar da kansu wajen yawon maula domin biyawa matansu bukatar da yafi karfinsu.
Zamu Ci Gaba.......................
0 Comments