Maza Suna Son Samun Wacce Zasu Aura Da Wadannan Dabi'un:


Maza Suna Son Samun Wacce Zasu Aura Da Wadannan Dabi'un:

SHARE 💕
#Tsangayarmalamtonga 

Ita mace ba kyauta ko matsayinta yake jawo mata ribibin masu sonta da aure ba. Halinta na kwarai suke sa mazan da suka san ciwon kansu suke fadi tashin ganin sun mallaketa.

Ga wasu halayen da maza suke bukatan samun su ga duk wata macen da suke sonta da aure.
 
1: Mace Mai Illimi: Maza suna some gano matakin illimin mace a addinance da kuma zamanance. Domin babu yadda mace zata iya yiwa abunda zata haifa tarbiya da jahilci. Wannan yasa ilimi shine abu na farko dake dauke hankalin maza da shi.

2: Tarbiya: Abu na gaba da duk wani namiji ke son ganin macen da yake so da shi bai wuce tarbiyanta ba.
Maza suna kula da yadda mace take mu'amala da mutane maza da mata. Irin kalaman dake fita daga bakinta, yadda take shiga idan zata fita da sauran dabi'u masu kyau. 

3: Macen Da Zata Yi Soyayya Saboda Allah: Sau tari mata sukan yi soyayya ne ba saboda ALLAH ba sai saboda wasu dalilan na neman abun duniya.
Duk macen da namiji zai fahimci tsakaninta da Allah take son shi, zai so ganin ya mallaketa a matsayin matarsa.

4: Mace Mai Sauki Kai: Maza suna son samun macen da zasu aura tana da sauki kai wajen yi musu biyayya.
Namiji bai son auren macen da take da kin ji da rashi saukin kai ba.

5: Fadin Gaskiya: Duk wata mace da take fadan gaskiya babu nuku nuku ko yaudara a lamuran ta takan sace zuciyar namiji.
Babu namijin da zai so ya auri mace mayaudariya ko makaryaciya.
 
Wadannan sune wasu daga abubuwan da mace suke son ganin mace dasu. Samunta da wadannan abubuwan na jawo mata farin jini da rabibin masu son aurenta.

Da fatan matan da suke da irin wadannan halayen zasu kara hakuri su kuma ci gaba da addu'a zuwa lokacin bayyanar mazan su na aure. Marasa hali irin wadannan su gyara halayensu.

Post a Comment

0 Comments