Matsalar Saurin Inzali Da Yadda Za'a Magance Ta.


Matsalar Saurin Inzali Da Yadda Za'a Magance Ta.


Ko ka san kashi 30 cikin dari na maza na fuskantar wannan matsala ta saurin kawowa maniyyi yayin saduwa da iyalinsu?

 To abin haka yake, kamar yadda aka wallafa a mujallar "The journal of the American medical association"
Sai dai abin damuwa anan shine duk da matsala ce da ke ciwa maza da yawa tuwo a kwarya,amma tattaunawa akan ta yakan zama wani abun damuwa, ba don komai ba, sai don al'adarmu, da mu ke daukar al'amura a matsayin na kunya ne koda ba na kunyar bane.

Wannan dalili ya sa mu rubuta makala akan wannan matsala don taimakawa masu fama da matsalar saurin inzali. Ba wani abu ya sa mu yin hakan ba sai don matsala ce da ke haifarwa mai ita matsananciyar damuwa. Mai irin wannan matsala na ganin ya gaza wajen biyawa iyalinsa bukatarta ta jima'i wanda hakan ka iya haifar musu da gagarumar fitina a rayuwar aurensu.



               
Me Ake Nufi Da Saurin Inzali ?

A takaice saurin inzali na nufin kawowa maniyyi da wuri ba lokacin da ake so ba. Mutum zai kasance mai saurin inzali idan yana fitar da maniyyi kafin ko da zarar ya shigar da azzakarinsa cikin farjin iyalinsa. Kai a wani lokacin ma ya kan yi inzalin ne tun lokacin ana gabatar da wasa.

Ita kuwa matsala ce da ke da ban haushi da ban takaici don kuwa tana hana miji da matar samun jin dadi da gamsuwa daga jima'i. Ko da yake masana a wannan fanni sun bayyana cewa wannan matsala ba abar damuwa ba ce tunda akwai hanyoyin magance ta. Kuma sun ce a wasu lokutan takan tafi bayan wani lokaci,amma dai bin wasu mataikai don gusar da ita da sauri zai taimaka.

Wannan matsala ta saurin inzali kan haddasawa ma'aurata jin haushin juna da kawo sabani a tsakanin su musammanma a lokacin da suka zo kwanciya.

Ana sanya mutum cikin masu saurin inzali idan: 

Yana kawo maniyyi minti daya ko kasa da haka da fara saduwa da iyali.

Idan ba zai iya dakatar da inzali ba yayin da yake saduwa da iyali.

Idan hakan ya haifar masa da matsananciyar damuwa da har ya ke gudun yin jima'i.


Me Ke Haifar Da Saurin Inzali ?.

 

Dalilaai da yawa ne ke haifar da wannan matsala, don haka babu wani abu guda daya da za'a danganta shi da saurin inzali don kuwa yana danganta ne daga mutum zuwa mutum.

Ga wadansu daga ciki, wadanda kuma su ne suka fi shahara wajen haifar da wannan matsala.

1. Sabon Shiga.

Idan mutum sabun shiga ne,barawo da sallama, Inji hausawa. Ga dukkan alamu wannan baya bukatar karin bayani. Amma dai muna nufin ango farkon aure.

 Kasancewar sa sabo ga al'amarin bai san yadda zai mallaki kansa ba yayin saduwa da amarya.


  2. Matsananciyar Damuwa.

Idan mutum ya samu kansa cikin damuwa, sakamakon al'amuran rayuwa, hakan kan haifar masa da matsala ta saurin inzali. Wannan kuwa ya hada da damuwa akan basussuka, gidan haya, matsalolin iyali,rashin lafiyar makusanci,durkushewar kasuwanci da dai sauran matsalolin rayuwa.

3. Daukar Lokaci Ba Tare Da Saduwa Ba.
Idan magidanci ya dauki lokaci mai tsawo ba tare da ya sadu da iyali ba, hakan kan haifar masa da saurin inzali.

4. Tsoro.

A duk lokacin da mai gida ya jewa iyali a lokacin da yake tsoron wani abu a rayuwa, ko kuma ya karaya akan ba zai iya biya mata bukata ba, to labudda yana iya kawo maniyyi da wuri.

5. Zumudi.
Wani lokacin idan mutum ya kasa mallakar kansa game da jima'i, saboda wani dalili to zai iya kawowa da wuri.

6. Gaggawa Yayin Jima'i.

Wanan na nufin mai gida ya dinga kaiwa da komowa cikin sauri a yayin jima'i. Ba shakka hakan na sabbaba saurin inzali.

7. Rashin Abinci Mai Gina Jiki.

Kullum dai muna fadar abincinka maganinka,masana na yawaita bada muhimmanci akan abincin da muke ci don kuwa shi ya shafi dukkan al'amuran lafiyarmu ne.


Fadakarwa: Wasu dalilan da ke haifar da saurin inzali cuta ce ko kuma wacce aka haifi mutum da ita.Ita kam irin wannan sai mai ita ya je ga likita don samun mafita.

Hanyoyin Magance Saurin Inzali.

Babban abin farin ciki game da wannan matsala shine,ana samun bakin zaren cikin sauki matukar dai ango ko magidanci zai bi shawarwarin masana.

Bayan haka ana bukatar hadin kan ma'auratan biyu don magance saurin inzali. Ba batun kunya a wannan fage.

1. Gabatar Da Wasa Kafin Jima'i.


Yana da kyau ango ko mai gida ya san cewa maza sun fi saurin yin inzali idan aka kwatanta su da mata, wannan yasa ya zama dole a gabatar da wasa kafin saduwa don a motsar mata da sha'awrta yadda za ku zo dai-dai lokacin inzali.

Ta yiwu wasu sun san yadda za su motsa sha'awar mace amma saboda sabin angwaye za mu kawo bayani a takaice.
Masana na ganin wasa kan fara ne tun daga maganganun fatar baki, kamar yabon irin kyaunta ko kwalliyarta da wasu kalamai da za su nuna kana sha'awar ta.

Idan an himmatu da yin jima'i akwai guraren da mace ta ke da matukar son a taba a jikin ta,ba don komai ba sai don suna da jijiyoyi da ke kaiwa kwakwalwa sakon jin dadi da sauri.

Ango zai mai da hankali wajen wasa da nononta sosai zai fara sannu a hankali, tun daga shafawa yana mulmula kansa,har ya kai bakinsa yana tsotsa..............

Sai gaban ta, a gaban ta kuma abin da ake kira da dan tsaka yin wasa da shi na saurin birkita mace. Don hakaa sai a kula ai wasa da shi ainun idan da halima a tsotse shi da baki.......

Daga nan za'a iya amfani da dan yatsa a saka cikin farji. Ai wasa dashi sosai. To wannan zai sa ta birkice.To anan sai ango ya lura a yayin da yaga ta birkice sosai tana bukatar sa, a wannan lokacin ne zai je mata, kuma hakan shi zai bayu ya zuwa ganin sun zo tare.

Idan kuma har ya riga ta, to ta yiwu itama ta kusa, kuma mun san ba da zarar namiji yayi inzali gabansa ya ke kwantawa ba,to zai raka ta kadan yana kaiwa yana komowa har itama ta biya bukatar ta.

Sai dai dole ne ango ya lura da inda yafi sa matarsa jin dadi don kuwa matan sun sha bambam. Inda zaka tabawa wata ta ji dadi ba lalle ne in ka tabawa wata za ta ji dadi ba.


2. Nesantar Da Al'aurarsa Daga Jikinta.

Idan har mutum na da saurin inzali,to yayin da suke wasa shi kuwa sai ya guji goga gabansa a jikinta hakanan kuma ita matar kar ta yi masa wasan. Ma'ana kar ta shafa ko taba gabansa har yayin da za su sadu.

3. Tsayawa Yayin Da Ake Jima'i.

A yayin da suke jima'i idan ya ji alamar zai yi inzali sai su dakata da abin da suke, hakan ya hada da daina motsi zuwa wani lokaci har sai ya ji ya koma, sai su ci gaba.

 Haka zai dinga yi har sai ya ga alamar ita kuma za tayi inzalin sai su yi tare ko ma ta riga shi. Saboda da wannan dalilin ne muka ambata a baya cewa al'amarin na bukatar hadin kan ma'auratan a junan su.

4. Motsa Jiki.

Bincike ya tabbatar da cewa motsa jiki da ya hada da sassarfa, gudu, da sauran wasannin motsa jiki na taimakawa mai wannan matsala ya samu waraka.
Karanta: Amfanin zuma ga lafiyarmu, a Qur'ani, Hadisi da binciken kimiyya.

5. Yanayin Kwanciya Lokacin Saduwa.

Yadda ma'aurata za su kwanta na da tasiri ta fuskar inzali. Bincike ya nuna amarya ta hau kan ango zai bayu zuwa ga saurin kawowarta. Ka ga idan haka ne, to lalle irin wannan kwanciya za ta taimakawa mai saurin inzali.

Shi ma wannan yana bukatar a gwada, idan an dace, to an samu mafita.

6. Jan Nunfashi Sannan A Sake Shi.

Mun fada a sama cewa dakatawa na kara tsawon lokacin kawowa. Hakanan a yayin da ake cikin jima'i sai a ja nunfashi ta hanci sosai ya shiga cikin ciki, sai a sake shi a hankali. Wannan ma na kawo jinkirin inzali.

7. Yin Jima'i A Hankali.

A guji gaggawa a yayin da ake jima'i da iyali. Abin nufi yayin da namiji ke kaiwa da komowa a kan iyali to yayi hakan a hankali,don kuwa zuwa da dawowa da saurin kan haifar da inzali ba tare da ka shirya ba.

Muna fata masu fama da wannan matsala za su jarraba bin wadannan hanyoyi don samu waraka daga wannan matsala mai tarwatsa rayuwar aure, kuma muna addu'a Allah Ya sa sanadiyar mu ne za su samu kubuta daga wannan matsala,amin.

A karshe muke tabbatarwa da ango ko magidanci cewa da zarar wannan matsala ta kau, hakika za ka ga canji, rayuwar aurenku za ta koma abar alfahari wacce ke cike da farin ciki,shakuwa da kuwa matsananciyar kauna.

Post a Comment

0 Comments