Irin Hiran Da Zaka Dauke Hankalin Budurwa Dasu:


Irin Hiran Da Zaka Dauke Hankalin Budurwa Dasu:

SHARE 💕
#Tsangayarmalamtonga 

A ci gaba da kawowa samari ko nace maza wasu dabarun shawo kan mata. A wannan darasin zai koyawa mazan yadda zasu shawo kan mace ta hanyar janta da hira.

Duk yadda kake son mace muddin bazata baka lokaci ba bazaka samu shawo kanta ba. Su kuma mata sai da dabaru ake iya samun hankalinsu harma su saurari mutum.
Ga wasu hiran da nan take zaka iya jawo hankalin mace dasu.

 
1: 🤳 Idan kana son jan hankalin mace ta hanyar jan ta da hira, zo mata da hiran abubuwan da suke faruwa a daidai wannan lokacin. Labarin daya mamaye gari ko kasa da kowa yake yi.
Idan ka fahimci tasan labari nemi ta sanar dakai abunda yake faruwa. Idan kuma ka fita sani lambarta mata.
Mata suna son jin labari, wannan yasa zata so jin labarin ga wanda yake da masaniya.
Kada ka sako mata da zancen soyayya a wannan lokacin. Amma dai ka nuna mata saboda matsayinta a wurinka yasa kake wannan hiran da ita.

2: 🤳 Kai tsaye nuna mata ta burgeka akan natsuwanta, kwalliyarta da dabi'unta.
Kace mata wannan ne ma yasa kake ta zumudin ku gaisa. 
Dauki lokaci mai tsawo kana mata bayanin abubuwan da suka burgeka game da ita. 
Mata suna son a yabesu. Hakan yasa suke sauraron duk wanda zai nuna musu kaunarsa garesu koda ba ta soyaya bane.

3: Idan 'yar bokoce zo mata da hiran boko da karfafamata akan karatu da kuma nuna mata irin matan da kake so kenan. Haka nan idan Islamiya take yi ka mata zancen tare da yi mata fatan alheri.
Mata suna son duk wanda zai karfafa musu gwaiwa akan abunda suke burin zama arayuwa. Wannan yasa zata baka kulawa tare da tuntubarka akan neman shawara neman fahimtar wani abu data kasa fahimta na karatu.

4: 🤳 Idan kana son jan hankalin mace ta hanyar hira da ita. Ka kirkiro hiran da zai saku yin musu da juna.
Ka musanta wani abunda ta fika gaskiya akai, koda wani za a tambaya shima ita zai goyawa baya.
Wannan musanta abunda ta san gaskiyansa da zaka yi, zata nemi ta dage sai ta gamsar da kai saboda tasan tana da hujja.
Mace muddin tasan tana kan gaskiyaryarta, ba zata taba hakura da hiran ba har sai wanda take musun da shi ya gamsu.

5: 🤳 Idan zaka zowa da mace da hiran yadda zata inganta rayuwarta domin cimma burinta. Zata ajiye komai datake yi domin sauraranka.
Mace duk lalacewarta, tana son taji ana bata shawarwarin da zasu amfaneta koda kuwa ba aiki dasu zata yi ba.
 
Ba duk mata bane suke son namiji yace musu yana sonsu kai tsayeba ba tare da ta fahimci akwai abunda yasa ka furta mata kalmar so ba.
Mace tana iya ganin gilmawar mutum kawai taji ta kamu da sonsa. Amma shi namiji yana kamuwa da son mace ce saboda wasu abubuwan daya gani tare da ita. Wannan yasa idan kacewa mace kana matukar sonta a haduwarku na farko bazata yarda ba.

Da fatan samari za a yi amfani da wadannan dabarun domin sace zuciyar wacce kake so.

Post a Comment

0 Comments