DAUSAYIN RAMADAN (DARASI NA


DAUSAYIN RAMADAN (DARASI NA 27.)

LAMUNIN SHIGA ALJANNAH

وعن عبادة بن الصامت رضي الله عنه أنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
 ((اضمنوا لي ستًّا من أنفسكم أضمن لكم الجنة:
1.اصدقوا إذا حدثتم،
 2. وأوفوا إذا وعدتم،
3. وأدُّوا إذا ائتمنتم،
4. واحفظوا فروجكم،
5. وغضُّوا أبصاركم،
 6. وكفُّوا أيديكم))
An ruwaito daga Ubadatu Ɗan Samit (RA) yace :

Manzon Allah saw yace: ku lamunce min yin abu shida zan lamunce muku shiga Aljannah. 
1. Ku faɗi gaskiya Idan za ku yi magana. 
2. Ku riƙe amana idan an amince muku.
3. Ku cika alƙawari idan kun ɗauka.
4. Ku kiyaye gaban ku (kada ku aikata alfasha)
5. Ku runtse idanuwanku (ga barin kallon haram)
6. Ku kamai hannayen ku (ga barin amfani da shi wajen cutar da jama'a.) 
(Al'imam Ahmad ya ruwaito da Alhakim da Baihaƙiy da Ibn Hibban. Shaikh Albany ya inganta shi.) 

Wannan hadisi ƙalubale ne gare mu, kowa ya auna kansa da shi ya ga inda yake da rauni domin gyara da samun wannan dama ta shi Aljannah da rahmar Allah.

Post a Comment

0 Comments