YIN UMRA A CIKIN WATAN RAMADAN KAMAR YIN HAJJI NE TARE DA MANZON ALLAH SAW.


DAUSAYIN RAMADAN (DARASI NA BIYU)

YIN UMRA A CIKIN WATAN RAMADAN KAMAR YIN HAJJI NE TARE DA MANZON ALLAH SAW. 

16. Yin umara a cikin watan Ramadhan daidai yake da kamar ka yi hajji tare da Manzon Allah ﷺ saboda hadisin Abdullahi Ɗan Abbas da ya ce, haƙiƙa Manzon Allah ﷺ ya cewa wata mace daga cikin mutanen madina da ake ce mata Ummu Sinanin “Me ya sa ba ki yi aikin hajji tare da mu ba? Sai ta ce, ya Ma’aikin Allah ﷺ muna da raƙuma (taguwoyi) guda biyu a gidanmu, ɗaya mai gidan namu ne ya tafi aikin hajji a kanta shi da ɗansa, ɗayar kuma ita suka bar mana a gida muke ban ruwa da ita. Sai Manzon Allah ﷺ ya ce mata, yin umara a watan azumi daidai yake da yin aikin hajji tare da ni.” A wata ruwayar ta muslim ya ce mata, “Ki je ki yi umara a watan Ramadhan domin yin umara a watan Ramadhan daidai yake da yin hajji tare da ni.” Haka kuma a wata ruwayar ta Bukhari sai ya ce mata, “Idan watan Ramadhan ya zo ki je ki yi umara a cikinsa, domin umara a cikin Ramadhan kamar hajji ce.” Amma fa ladan hajjin ake samu ba wai farillar hajjin ce take sauka daga kan wanda bai yi ta ba.
 17. Wanda ya yi azumin watan Ramadhan yana daga cikin siddiƙai da shahidai, saboda hadisin Amru Bn Murra Al-Juhani ya ce, wani mutum ya zo wajen Ma’aikin Allah ﷺ daga ƙabilar ƙudha'a, sai ya ce, ya Manzon Allah ﷺ ka bani labari idan na shaida babu abin bautatawa da gaskiya sai Allah, kuma na shaida Annabi Muhammadu ﷺ Ma’aikin Allah ne, nayi salloli biyar, na ba da zakkah, sannan nayi azumin watan Ramadhan ni waye? Sai Ma’aiki ﷺ ya ce, “Kana cikin siddiƙai da shahidai.”
18. Haka kuma yin azumin watan Ramadhan yana jawo wa mutum shiga aljannah saboda hadisin jabir
  18. Yin ƙiyamul laili a cikin watan Ramadhan da imani da neman lada ana gafarta zunubi da shi, saboda hadisin Abu Hurairah da ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Wanda ya yi tsayuwar Ramadhan da imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na daga zunubansa.”
19. Watan Ramadhan wata ne na sallar tarawihi, ita kuma sallar tarawihi sallah ce wadda ba a yin ta sai a cikin watan Ramadhan, saboda hadisin Ummina Ai’shah RA. ta ce, Manzon Allah ﷺ ya fito a cikin tsakiyar dare sai ya yi sallah a masallaci sai mutane suka bishi wannan sallar sai aka wayi gari ana ba da labarin wannan sallar da Ma’aiki ﷺ ya yi a cikin dare, da dare na gaba ya zo sai mutane suka taru fiye da dare na farko, sai ya yi sallah da mutanen sai aka wayi gari labari ya ci gaba da yaɗuwa, sai dare na gaba ya zo mutane suka sake taruwa a wannan daren fiye da na baya sai Manzon Allah ﷺ ya yi musu sallah, a dare na huɗu sai masallaci ya cika da jama'a sai Ma’aiki ﷺ bai fito ba, har mutane suka ce lokacin sallah ya yi, Manzon Allah ﷺ bai fito ba, har sai da lokacin sallar asubah ya yi. 
Bayan an yi sallar asuba sai Ma’aiki ﷺ ya fuskanci mutane ya yi godiya ga Allah ﷻ ya yi kirari a gare Shi, sai ya ce, bayan haka ya ku mutane al'amarin ku bai buya a gare ni ba, sai dai na ji tsoron kada a wajabta muku wannan sallah ne ku kasa yin ta shi ya sa ban fito ba.” Wannan kuwa ya faru ne a cikin watan Ramadhan.
20.Wanda ya yi sallar tarawihi tare da liman sannan kuma ya lazimci wannan jam'in har sai da liman ya ƙare sallar za a rubuta masa lada kamar ya yi tsayuwar daren ne gaba ɗayan sa. Saboda hadisin Abu Zarrin da ya ke yin bayani game da tsayuwar watan ramdhan, sai ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Wanda ya tsaya tare da liman suka yi sallar tarawihi har aka gama, to za a rubuta masa kamar ya tsaya a gaba ɗayan wannan daren ne yana sallah.” A wata ruwayar kuma ya ce, “Za a rubuta masa ya tsaya da sallah a wannan daren dukkansa.”
Za mu ci gaba insha Allah.

Post a Comment

0 Comments