Wasu Abubuwan Da Zasu Takaitawa Masoya Yawan Samun Sabani:


Wasu Abubuwan Da Zasu Takaitawa Masoya Yawan Samun Sabani:

SHARE 💐
#TsangayarMalam 

Dole a samu sabani ko rashin fahimta tsakanin ma'aurata da masoya. Sai dai hakan bai zama matsalar da zai hana ma'aurata da masoya daukan matakin da zasu kaucewa hakan ba.

Ga wasu matakan hana yawan samun sabani tsakanin masoya da ma'aurata.
 
1: Domin rage yawan samun Sabani a tsakaninku, yana da kyau duk wanda yayi ba daidai ba cikinku ya amsa laifinsa kuma ya bada hakuri.

Babu sauran wani hayaniya ga duk lokacin da wani mai laifi ya amsa laifinsa kuma ya bada hakuri.

Ta hanyar yadda da laifi da Bada hakuri ma'aurata da masoya zasu samu saukin yawan samun sabani a tsakaninsu. 

2: Domin samun saukin wajen rashin fahimta tsakanin ma'aurata da masoya yana da kyau su rika sauraran junansu.
A duk lokacinda guda yake da wani korafi, guda yayi hakuri ya saurare shi domin samo hanyar da zasu magance matsalar.

3: Cikin gaggawa yana da kyau ma'aurata ko masoya su magance matsalar data kunno kai dake jawo musu sabani ko rashin fahimtar junansu. 
Saurin daukan matakin akan matsalar dake jawo muku matsalar zai iya kawo karshen matsalar da kuke samu.

4: Kada ma'aurata ko masoya su zama masu Kullatar juna a rai. Nan take idan anyi abu, aka kuma samu fahimta to a yafewa juna a manta aka kuma kiyayi gaba.
Hakan zai rage yawan samun sabini da rashin fahimtar da kuke iya samun ko kuke samun a mafi lokaci idan za a yafewa juna.

5: Kada ma'aurata ko masoya su yiwa junansu fahinta na hankali da tunaninsu zai iya zuwa daya.
Shi namiji ako yaushe ya dauka cewa ba lalle bane abunda ya dace ayi shine macen da yake aure ko yake soyayya da ita zata yi ba.

Wani lokacin mutum yana so a masa tuni ko a nuna masa mahimmancin yi ko rashin yin wani abun.

Idan ma'aurata da masoya zasu yiwa junansu uzurin cewa ba lalle bane su iya zama daya wajen hankali da tunani. Tabbas ana iya samun saukin wajen rashin fahimta tsakanin su. 

Da fatan za a rika hakuri da juna domin samun zaman lafiya da walwala tsakanin masoya ko ma'aurata.

Post a Comment

0 Comments