Kalaman Soyayya Karanta Zafafan Kalaman Soyayya Na Barka da Shan Ruwa A Lokacin Azumi:
{NA MAZA}
1} Fatan gushewar yunwa da sanyayar
ruhi da tabbatuwar lada ga wadda
tinaninta ke ɗebe min kewa a lokacin da nake galabaice ko a lokacin da nake tsaka da hutawa. Fatan Kin Sha-ruwa Lafiya?
Marubuci: Abba Muhammad Dan Hausa
2} Kasancewar ki a tare da ni, ya sa ni jin kaina a matsayin wani mutum mai daraja ta musamman. Ina son ki, so irin wanda kalmomi ba zasu iya bayyanawa ba. Barka Da Shan-ruwa.
3} Na kasance cikin murnar zagayowar
watarana, wato ranar da kika nuna
amincewarki ga soyayyata. Ba na jin zan iya rayuwa ba tare da ke ba, saboda ke ce rayuwata, kuma ke ce mahaɗin
numfashin da nake shaka. Barka Da
Hutawa.
4} Na kan yi mamaki a baya, a duk
lokacin da na ga wani ya shiga
matsananciyar damuwa a kan so, amma bayan haɗuwata da ke, na fahimci abin da ake kira da so. A halin yanzu, ni ma a shirye nake da na yi yaki da duk wanda ya yi kokarin raba ni da ke. Barka Da Shan-ruwa.
5} Matukar zan cigaba da kasancewa a
tare da ke, ba na jin hatsarin da nake ji
ana cewa so yana da shi zan gamu da shi watarana. Ke ta daban ce kuma ta
musamman a cikin rayuwata. Ina Son Ki.
6} Kamar yadda zai yi wuya mutum ya
manta da wani ɓangare na jikinsa, haka
ni ma zai yi wuya na manta da ke a
rayuwata. Kin shiga zuciyata kin zauna,
kin bi jijiyoyin jikina kin narke a cikin
jinina. Ina Son Ki. Barka Da Shan-ruwa.
7} Burina a yanzu, bai wuce ganin na
mallaki tauraruwar da haskenta ke haske sararin samaniya ba, a kowane dare. Wadda nake fatan ta haskake rayuwata da haske mara disashewa. Ke ce dai wannan ɗin nan, wadda ke bayyana a cikin baccina, ko a lokacin da nake farke, da rana ko a cikin dare. Ina Son Ki.
8} Fatana a ko da yaushe, na gan ki cikin walwala da nishaɗi. Burina na ga fuskarki cike da fara’a da annushuwa. Fatan Kin Sha-ruwa Lafiya.
9} Ki kalli sararin samaniya, za ki gan ni tsaye a kusa da ke, domin kuwa, ni ma na yi hakan kuma na gan ki a kusa da ni, haskenmu na haska duniya. Ina Fatan Kin Sha-ruwa Lafiya? Na yi Kewar Ki.
10} Me zai hana ni kasancewa tare da
wadda ta mallaka min zuciyarta? Wadda nake da tabbaci kan yadda take gudun ganin na shiga damuwa? Wadda ke tattalin farin-cikina? Wadda sautin
muryarta ke cire min kasala da sanya ni
yin bacci mai cike da mafarkai masu
daɗi? Ba kowa ba ce wannan face ke! Ina Son Ki. Barka Da Shan-ruwa.
11} A dukkan lokacin da muka yi nesa da juna, na kan ji da ma a ce akwai manyan tsaunika a kusa da ni, da na hau ko zan samu na hango murmushin fuskar nan taki mai taushi. Na Yi Kewar Ki.
12} Wasu na gulmar, wai watarana za a
wayi gari na ji son ki ya ragu a cikin
zuciyata, idanuwana su daina ganin
kyawunki, ni kuwa na ce, ba na fatan
zuwan wannan rana ina mai numfashi a doron ‘kasa. Ni a kullum, ina jin sonki ne na karuwa a cikin zuciyata, a dukkan lokacin da muke tare ko muka nesanta da juna. Ina Son Ki.
13} Na ji tsoron mafarkin irin
mummunan halin da zan shiga a duk
lokacin da na rasa ki. Zamowa ta
cikakken mutum zai kammala ne a ranar da kika zama mata a gare ni. Ina Son Ki. Yaya Ibada?
14} Haɗuwarmu ta kasance ne bisa
kaddara, zamowar mu masoya ya faru ne bisa zaɓinmu, amma ba wa son ki gurbi a cikin zuciyata, ya zama dole ne a gare ni, saboda kin zamo wani ɓangare na rayuwata, haka kuma tinaninki ya zama masarrafin sarrafa akalar rayuwa da tinanina. Ina son ki, so irin wanda gangar jiki take yi wa ruhi. Barka Da Shan-ruwa.
15} Yunkurin sanin adadin yadda nake jin son ki a cikin zuciyata, da dalilan da suka saka nake kaunar ki, a gare ni, daidai yake da a ce na bayyana irin ɗanɗanon da ruwa yake da shi ne a cikin baki. Tabbas abu ne mai matukar wahala. Fatan Kin Sha-ruwa Lafiya.
16} Kina da dabaru na sanya ni yin
murmushi ko da a ce ina cikin fushi ne.
Kin zamo wata ta-daban a gare ni. Ina
son ki, so mara iyaka. Barka Da Hutawa.
17} Kina da kyau masoyiyata, fiye da
yanda kike gani a madubi. Kyawu ne irin wanda babu wani furuci ko zanen wani mai zane da zai iya fasalta shi. Ina Son Ki. Fatan Kin Sha-ruwa Lafiya.
18} Ina fatan mafarkin da na yi jiya, ya
maimaita kansa a cikin baccina na yau,
mafarkin da nake fatan ya zamo gaskiya, mafarki ne da a cikinsa na gan mu a tare a matsayin miji da mata. Barka Da Hutawa.
19} Ganin shigowar sakonki cikin wayata, na canja yanayin da nake ciki daga damuwa zuwa farin-ciki, ba komai bane ya jawo hakan face tsantsar son ki da ke killace a cikin zuciyata. Ni ne dai naki a kullum…..
20} Kafin na haɗu da ke, kalamaina na da saukin samuwa ga kowace mace, amma a halin yanzu babu wata mace daga cikin jerin ‘yammatan birni ko na karkara da zata samu irin kulawar da na shirya ba ki a tsawan rayuwar zamantakewarmu, daga yanzu har izuwa karshen rayuwata. Ke ce wadda na zaɓa, nake fatan mu kasance tare har abada. Ina Son Ki.
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
{NA MATA }
1} Zuwa ga zaɓin zuciyata, ina fatan ka
sha ruwa lafiya? Ina fatan izuwa yanzu
nutsuwa ta game jikinka, ishiruwa ta
gushe daga makoshinka? Ina kuma fatan lada ya tabbata a gare ka. Fatan ka sha ruwa lafiya? Ka Huta Lafiya.
2} A dukkan lokacin da na ga daren
Lailatilkadari, zan kasance mai rokon
Ubangiji Ya mallaka min kai a matsayin
mijina uban ‘ya’yana, ina fatan kai ma
zaka kasance mai tsawaita tsayuwa cikin kowane dare domin ganin cikar
burinmu? Ina Son Ka.
3} A lokuta da wurare daban-daban ina
ganin ka kana yi min gizo, ina ganin ka a lokacin da idanuwana ke a rufe ko a
buɗe. Ba na iya yin komai ba tare da
tinaninka ba. Fatan Ka Sha-ruwa Lafiya.
4} Jin muryarka na sakwan guda, na jefa ni cikin kogin tinaninka, na tsawan
lokacin da idanuwana ke kasancewa a
buɗe. Barka Da Shan-ruwa.
5} Irin kulawar da kake nuna min a
kullum na saka ni tinanin irin yadda
rayuwarmu za ta kasance a nan gaba. Zanbzamo tamkar sarauniya a gidanka, kai kuma zaka zamo sarkin da babu wani mai irin masarautarsa a duniya ta kowace fuska. Ina Son Ka.
6} Zuciyata ba za ta taɓa canja matsayin
da kake da shi ba a cikinta. Murmushina gare ka ba zai taɓa yankewa ba. Son ka a cikin zuciyata ya yi kafuwar da ba zai taɓa goguwa ba a cikinta na har abada. Barka Da Hutawa.
7} Da a ce zan iya zama komai, da na
zama ruwan hawaye a gare ka, a haife ni a cikin idanuwanka, na rayu a saman
kumatunka, na mace a saman laɓɓanka. Ina son ka so mara misaltuwa. Barka Da
Shan-ruwa.
8} A dukkan lokacin da kake bukatar
wani ya taya ka hira, karda ka manta
kana da ni, ka nemo ni domin ɗebe maka kewa a cikin kowane irin yanayi da lokaci. Fatan Ka Wuni Lafiya? Yaya
Ibada?
9} A lokacin da na tino irin rayuwar da
na yi a baya, na kan hango irin asarar da na yi, na kasancewa ta ni kaɗai ba tare da kai ba , yanzu na same ka, ina ji na a matsayin wata wadda ta fi kowace mace sa’a a rayuwa. Ina fatan na kasance a tare da kai na har abada. Barka Da Shan-ruwa.
10} Ba zan taɓa mantawa da ranar cikar burina ba, ranar da wanda nake so ya nuna min soyayyarsa a fili, ba kowa bane face kai hasken idaniyata. Ina son ka. Barka Da Hutawa. Fatan Ka Sha-ruwa Lafiya?
SAKO MAI MUHIMMANCI
Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko'ina wato Allah. A kiyaye haƙƙin mallaka, a guje wa satar fasaha.
0 Comments