DAUSAYIN RAMADAN (DARASI NA 22)


DAUSAYIN RAMADAN (DARASI NA 22)

LADUBBAN ADDU’A DA SHARUƊƊANTA DA KUMA ƘA’IDODINTA

Malamai sun ce akwai abubuwa guda tara (9) da aka fi so mutum ya mai da hankalinsa ya kula da su ya yin roƙo da addu’a , sune kamar haka: 
 1- Ya riƙa roƙon Allah ﷻ shiriya, wato duk addu'ar da z aka yi, ka roƙi Allah ﷻ ya shiryar da kai domin falalarsa. 
2- Ya roƙi Allah ﷻ gafarar zunubbansa manya da ƙanana, na fili da na ɓoye, waɗanda ya sani da waɗanda bai sani ba. 
3- Ya roƙi Allah ﷻ ya ba shi aljanna, ya tseratar da shi daga shiga wuta. 
4- Ya roƙi Allah ﷻ ya ba shi lafiya da zama lafiya a duniya da lahira da ciki ƙabarinsa.
 5- Ya roƙi Allah ﷻ ya tabbatar da shi a kan addininsa har zuwa lokacin fitar ransa da lokacin tashinsa a filin ƙiyama.
 6- Ya roƙi Allah ﷻ ya ba shi kyakykyawan ƙarshe a cikin lamarinsa gaba ɗaya, wato ya gama da duniya lafiya. Ya roƙi Allah ﷻ ya gyara masa duniyarsa da lahirarsa. 
7- Ya roƙi Allah ﷻ ya dawwamar masa da ni'imarsa. ya kuma amintar da shi daga gushewarta a gare shi. 
8- Ya roƙi Allah ﷻ ya tsare shi daga faɗawa cikin tsananin bala’i da musiba a duniyarsa da lahriarsa, ya kuma tsare shi riskar taɓewa da asara da mummunar makoma da kuma dariyar maƙiya.
9 ya roki Allah ya yi wa iyayan sa gafara, da Malaman sa da ƙasar sa ya roƙa mata lafiya da zaman lafiya da shugaban ci na gari.

Post a Comment

0 Comments