Amfanin Ganyen Mangwaro 10 A Jiki Da Yadda Za A Sarrafa Shi


Mangwaro na daga cikin ‘ya’yan itatuwan da ake ci wanda ya kunshi sinadarorin inganta kiwon lafiyar al’umma.

A cikin mangwaro akwai ‘Bitamin C wanda ke warkar da Mura, Rauni da dai sauran su, sai kuma akwai copper wanda ke kare mutum daga kamuwa daga cututtuka, potassium kuma wanda ke inganta motsa jiki da magnesium wanda shi kuma ke kaifafa kwakwalwa.

Bugu da kari kuma likitoci sun bayyana cewar ganyen mangwaro ma na dauke da sinadarorin dake inganta kiwon lafiyar mutum.

Bayanai sun nuna cewar a nahiyar Asiya sun fi yin amfani da ganyen mangwaro wajen warkar da cututtuka saboda ingancin da yake da shi.

Ga amfani goma da ganyen yake da shi

Ganyen mangwaro na kawar da cutar sikari wato ‘Dibetes’

Ganyen mangwaro na warkar da cutar sikari ne idan aka shanya shi ne ya bushe bayan nan kuma akan jika garin a ruwa sai a rika sha.

Yana yin maganin hawan jini.

Ana yin amfani da garin busasshen ganyen mangwaro, sai a rika diba ana dafa shi ana sha kamar shayi. Hakanan kuma zai taimaka wajen kawar da hawan jini.

Yana warkar da cutar koda

Shan ruwan ganyen magwaro da aka jika na warkar da cutar koda.

Yana warkar da matsalolin da ke hana yin numfashi.

Idan aka hada ruwan ganyen mangwaro da zuma, ana samun lafiya ga Mura da kuma cutar Asma.

Ya na kawar da atini.

Shi ma idan aka sha ruwan zai taimaka wajen dakatar da cutar Atini.

Ya na dakatar da shakuwa.

Wanda ya ke fuskantar matsalar shakuwa zai warke idan ya shaki hayakin ganyen mangwaro.

Haka nan ma mai fama da rashin natsuwa wato ‘Andiety’ yana iya samun sauki idan yana shan ruwan ganyen mangwaro.

Mai fama da ciwon ciki zai sami sauki idan yana shan ruwan dafaffen ganyen ko wacce rana da safe kafin a ci abinci.

Ya na warkar da ciwon kunne.

Ruwan dake cikin ganyen mangoro ya kunshi sinadarin warkar da ciwon kunne wanda idan aka diga a kunnen dake ciwo zai warke.

Ganyen mangwaro na warkar da kuna

A na amfani da tokar ganyen mangwaro a shafa a kan rauni don a warke.

Post a Comment

0 Comments