Abubuwan Kiyayewa Cikin Ramadan
Assalamu Alaikum, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya sa mu ga karshen wannan wata lafiya, kuma Ya sa mu dace da dukkan alheransa, amin.
Ga bayani mai dauke da amsoshin tambayoyin da wasikun ku da ka aiko game da yanayin mu’amula tsakanin ma’aurata a cikin wannan wata na Ramadan, wato abubuwan da suka dace da wadanda ba su dace ba, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Abubuwan Da suka halatta:
1.Ba laifi rike hannun juna, rungumar juna ko sumbatar juna tsakanin ma’aurata da rana in dai yin hakan ba zai motso masu da sha’awa ba, domin Ummuna A’isha RA ta fada cewa Annabi SAW yana yin hakan, amma sai dai SAW ya zarce kowa wajen karfin halin danne da tsare sha’awarsa; saboda haka sai a kiyaye sosai, in an tabbatar akwai yiwuwar motsuwar sha’awa komin kankantarta, to sai a kauce wa yin hakan, da fatan Allah Ya ba da ikon kiyayewa, amin. Ya ’yan uwa mu lura da muhimmancin wannan ayyyuka cikin rayuwar aure, ta yadda har ga shi Annabinmu SAW, daukar azumi bai sa ya daina yin su ba, saboda mahimmancin su. Mu kuwa al’ummar Hausawa ko ba cikin azumi ba ne ba’a yin su, kuma su ma din Sunna ce kamar yadda Sallolin Nafila suke Sunna, sai ya kasance ma’aurata ba su taba juna sai lokacin ibadar aure kadai, rashin irin wannan ne ke sa ma’aurata su zama kamar ba ma’ auratan ba, ba wani irin kusanci da shakuwa na musamman tsakaninsu. Da fatan za mu fara rayar da wannan sunna daga wannan wata, ya kasance ana rike hannu, runguma da sumba amma na isar da so, kauna da kulawa ba na motsar da sha’awa ba.
2. Maganganu da wasu dabi’un nuna soyayya da rana ba haramun ba ne in dai hakan ba zai motso da sha’awa ba in kuma ma’aurata sun tabbatar za su iya danne sha’awar su.
3.In asuba ta riski ma’aurata da janaba, azumin su na nan, kuma ba laifi yin sahur cikin janaba, haka kuma ba laifi don sun jinkirta wanka zuwa lokacin da rana ta fito, amma ya fi kyau su yi wankan nan da nan don yin Sallah cikin lokacinta, kuma don Mala’ikun Rahma su samu kusantarsu.
Abubuwan Da suka Haramta:
1.Kowa dai ya san matsayin yin ibadar aure da rana lokacin Ramadan, babban alkaba’ir ne, kuma bayan rama azumin sai an yi kaffara da azumi 60 ga duk dayan da aka bata ta wannan hanyar.
2. Ga ma’auratan da suka aje azumi saboda lalurar tafiya, shayarwa ko rashin lafiya, bai kamata gare su yin ibadar aure da rana ba, ya fi kyau su kame don girmama wannan wata mai alfarma.
3. Ma’aurata su kauce yin duk wani abu da zai motso da sha’awar junan su, ba laifi yin kwalliya ko sa turare ko kunna turaren kamshi na wuta da rana, amma in hakan zai motso da sha’awar juna sai a kauce wa yin hakan.
4· Fitar da maniyyi a ido biyu sai an rama azumin, in kuma aka fitar da shi da gangan ta dalilin zinar hannu ko ibadar aure to sai an rama azumin tare da kaffara.
Abubuwan Kiyayewa:
1. Fitar da maziyyi ko wadiyyi bai karya azumi sai dai a tsabtace wajen a yi alwalla, haka ma fitar maniyyi a dalilin mafarki da rana bai karya azumi, sai dai a yi wanka a ci gaba da ibada.
2. Ma’aurata a dage da yin hakuri da juna cikin wannan wata, maigida ya yi hakuri kar ya yi fushi da uwargida don ba ta hada abincin buda baki da wuri ba, kar kuma ya matsa mata da dole sai ta girka sabon abinci lokacin sahur, Uwargida kuma a kara dagewa, kar ki bari aikin gida ya hana ki yin ibadar ki cikin lokacin ta, ki sani hakkin Allah a kan ki yana sama da hakkin iyalin ki ko na ke kan ki. Da fatan Allah Ya sa mu dace amin.
Zan dakata a nan, sai mako na gaba in Allah Ya kai mu, da addu‘ar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.
0 Comments