Yadda Zaki Bambamce Dattijo Da Yaro Tsakanin Masu Sonki Da Aure:


Yadda Zaki Bambamce Dattijo Da Yaro Tsakanin Masu Sonki Da Aure:

SHARE 💞
#TsangayarMalam 

Akwai mutanen da suke da karancin shekaru, amma muamalarsu da mutane irin na Dattawa ne. Akwai kuma masu yawan shekaru amma halayensu da dabi'unsu irin na yara ne.

Ga wasu halayen da sai namiji mai halin yarinta kadai yake aikata su.
 
Yadda zaki fahimci da yaro kike soyayya shine. Yau zai nuna miki ya damu dake. Gobe kuma sai ya dauke miki kafa sai kuma ranar daya bushi iska sannan zai ci gaba da soyayyar.

Muddin kika fahimci haka wajen mai sonki, komai shekarunsa to yaro ne a fanni na soyayya.

Maza masu halin yarinta a soyayya sune da zaran sun soma soyayya da mace, zasu bukaci ta tura musu hotunan tsiraicinta.
Muddin kika fahimci haka wajen namijin dayace yana sonki da aure, to ba Dattijon namiji bane yaro ne.

Samarin yara sune suke yadawa abokai mu'amala na sirri da sukayi da masoyansu.

Da zaran kinji labarin wani abu na sirri da kuka fada ko kukayi a bakin wasu da suka ji daga wajen masoyin ki, to wannan masoyin naki yaro ne ba Dattijo bane.

Dattijon namiji idan yana soyayya da mace burinsa shine suyi aure ba tare da daukan lokaci mai tsawo ba.

Shi kuwa aro a kullum uzuri yake bijirowa dashi. Zancen aure ma sai idan kece kika dauko maganar kamin kayi.
Wannan alama ne karara dake nuna kina soyayya ne da yaro.

Yawancin yara a soyayya basu da ra'ayin kansu sai abunda Hajiya tace. Muddin kika ji mai sonki na yawan ambatar Hajiya kamin ya gudanar da wani abu a rayuwarsa to fa kin fada soyayya ne da yaro.

Samarin yara a kullum suna ganin alfarma suke yiwa macen da suke soyayya da ita. Hakan yasa duk yadda zai bata miki rai ba zai taba baki hakuri ba. Kuma bai damu ya miki wulakanci a gaban mutane ba.

 Babban abunda ke gaban Yaron saurayi bai wuce holewa ba. A kullum banda zancen fati da suka shiryawa 'yan matansu na bariki da shirin fita gidan rawa a duk dare babu abunda ke gabansa.
Kina fahimtar haka a wajen mai sonki da aure tofa kin fada hannun yaron saurayi.

Dattijon namiji bazai taba miki alkawarin da bazai cika ba. Haka nan babu karya ko yaudara a tsakaninku.
Amma shi yaron saurayi kalamansa 10 duk 9 Babu na gaskiya. Ga alfaharin tsiya da gadara.

Akasarin samarin yara basa son neman na kansu. Sunfi sha'awar idan 'ya'yan masu kudi ne a Basu su kashe. Idan kuma yaran talaka ne kullum suna gindin yaran masu kudi ko wajen da zasu yi maula amma ba inda zasuyi aiki su samu ba.

Wadannan wasu daga cikin yadda mace zata bambamce tsakanin Dattijon Namiji Mai Sonta da aure da kuma Yaro.
Da fatan mata zasuyi amfani da zahiri wajen tace namenan aurensu.

Post a Comment

0 Comments