Niyyar Aure: Kwadaitarwa Ga Matasa
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Assalamu Alaikum Malama Nabila,
Ni dai Wallahi ina son rayuwar aure, kuma ina so in yi aure, sai dai ni matashi ne kuma dalibi, ba ni da kudin neman aure; ga shi na matsu da son aure a dalilin matsananciyar sha’awa da ke damu na. Don Allah ki ba ni shawarar da za ta karfafa mini gwiwa.
Na gode;
In sha Allah ga bayani da zai karfafa maka gwiwa tare da sauran matasa har ku garzaya ku fara kokarin zama magidanta. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da duk masu bukatarsa, amin.
Sanin muhimmancin Aure: Ya ku ’yan uwa matasa! Ku sani, aure gagarumar ibada ce mai matukar muhimmanci; mai cike da alherai da darajoji marasa iyaka. Ibada ce mai tsananin girma ta yadda har Annabi SAW ya bayyanata da cewa ‘rabin addini ce.’ Haka kuma Umarnin Allah SWT ne kuma umarnin Manzon Allah SAW ne, kuma daga cikin mafi soyuwar sunnoni gare Shi SAW.
Don haka rashin kudi ko kasancewa a cikin halin neman ilmi ba zai hana yin aure kuma ba zai haifar da matsala bayan an yi aure matukar matashi ya kyautata niyyarsa, kuma ya bi ka’idojin da addinin musuluncin ya gindaya yayin neman aure da bayan yinsa. Mu tuna cewa Annabi SAW Ya daura aure ga Sahabinsa RA a lokacin da ba shi da komai sai mayafin jikinsa kadai akan sharadin cewa zai koyar da ita Ayoyin Al-kur’ani a matsayin sadakinta.
Akwai masu tunanin cewa ai zamani ya canza, yanzu aure dole sai da kudi, wannan kuskure ne; domin addini daya ne; kuma canzawa ko gurbacewar zamani bai isa ya canza Umarnin Allah SWT da na ManzonSa SAW ba. Kuma duk matashin da ya kyautata niyyarsa ya bi dukkan ka’idojin addinin Musulunci, lallai Allah Zai taimake shi ya yi auren ko da ba shi da kudin, bayan aure Allah Ya yi alkawarin cewa zai wadata matalautan da suka yi aure daga falalarsa. Ga kadan daga cikin alherai da darajojin aure don kara kwadaitar da matasa da gwauraye don su garzaya su fara shirin zama magidanta.
1. Taimakon Allah Ya Tabbata A kan Mai Neman Aure: Kamar yadda aka ruwaito daga Manzon Allah SAW cewa: “Mutum uku sun cancanci taimako daga Allah Madaukaki, wadannan su ne: Wanda ya yi aure domin tsare farjinsa; bawan da ya kulla alkawari don fansar kansa daga ubangidansa da kuma wanda ya tafi yaki don daukaka kalmar Allah SWT. Don haka duk mutumin da ya kai munzilin yin aure yana da kyau ya dauri aniyar yin auren nan kada ya ce sai lokaci kaza, ko sai ya gama kaza, in dai mutum ya kyautata niyyarsa, to Allah Zai taimake shi kuma zai bude masa kofofin arziki daga inda ba ya zato, domin Allah ba Ya saba alkawari.
2. Budewar kofofin Arziki: Allah SWT Ya yi umarni ga wannan Al’umma da cewa: “Ku auri gwauraye daga cikinku kuma da salihai daga bayinku da kuyanginku. Idan sun kasance matalauta, Allah Zai wadatar da su daga falalarsa. Kuma Allah Mawadaci ne, Masani.” Don haka wannan albishir ne ga duk masu niyyar yin aure daga Allah Madaukakin Sarki cewa lallai Zai azurta su daga falalarSa a dalilin yin aurensu. Wannan ne ma ya sa wasu daga cikin Sahabban Manzon Allah Radiyallahu Anhum an ruwaito suna masu fadakar da mutane cewa su nemi arziki ta hanyar yin aure, domin Allah Ya fada cewa zai azurta duk wani matalauci bayan ya yi aure.
3. Rabin Addini: Manzon Allah SAW Ya fada cewa duk mutumin da Allah Ya nufa da yin aure, to ya cika masa rabin Addininsa; don haka sai yaji tsoron Allah a daya rabin. Daga wannan bayani na Manzon Allah SAW, muna iya fahimtar cewa aure kamar wani ganuwa ne mai bayar da tsari ga imanin Mumini; domin yana karewa daga fada wa ayyukan sabon Allah masu yawa, wadanda za su iya nakasa imani har mutum ya wayi gari ya bata rabin addininsa, ga shi kuma bai mallaki daya rabin ba, watau shi ne aure.
Don haka duk wani Musulmi na kwarai mai fatan cin nasara a duniya da Lahira, yana da kyau ya gaggauta rabuwa da zaman gwauranci ya yi kokarin yin aure.
4. Cikar Kamalar dan Adam: Ko min girman matsayi da nisan dattijantakar mutum, to daraja da kamalarsa ba su taba cika a idon mutane matukar bai taba aure ba; ko kuma yana zaune haka nan ba mata. Kuma komai karantar shekarun matashi, in dai yana da aure to zai kara masa mutunci da daraja a idon mutane.
Don haka sai matashi ya mutunta kansa, kuma ya cika kamalarsa ta hanyar yin aure.
5. Aiki Da Umarnin Allah SWT Da ManzonSa SAW: Duk wanda ya yi aure, to yana cikin yin biyayya ne ga umarnin Allah SWT kamar yadda ya zo a cikin Ayar da ta gabata a sama, sannan a Hadisai daban-daban, Manzon Allah Ya yi umarni da yin aure domin dacewa da albarkokin da ke cikinsu; muhimmai daga ciki su ne cikar al’ummar Musulmi da kuma more jin dadin mu’amula irin ta aure.
0 Comments