Idan Har Kina Son Sanin Inda Namijin Dake Sonki Ya Sa Gaba Game Da Soyayyar Ku Samu Amsar Wadannan Tambayoyin Cikin Hikima Daga Gareshi:


Idan Har Kina Son Sanin Inda Namijin Dake Sonki Ya Sa Gaba Game Da Soyayyar Ku Samu Amsar Wadannan Tambayoyin Cikin Hikima Daga Gareshi:

SHARE 👤
#TsangayarMalam 

Ba komai ke jawowa mata fadawa hannun maza mayaudara cikin sauki ba irin yadda da zaran sun fada son namiji basu damu su fahimci alkiblar namijin ba har sai bayan daya yaudareta ya tsaire daga wannan lokacin ne kuma zata soma habaice habaice su namiji ba Dan goyo bane. Namiji gumba, namiji Maci amaba da dai sauran bakaken zantuka da suke fadawa maza bayan kashi 60 na damar yaudaran da aka mata an samosu daga wajenta ne ba.

Yiwa namijin da yace yana sonki da aure wadannan tambayiyin cikin hikima. Ki kuma natsu kiji amsar duk tambayar da zaki masa domin yankewa kanki hukunci game da shi.

 
1: Tambayi mai sonki wacce irin mace yake burin ya aura a rayuwarsa.

2: Ki Nemi Sanin Nan Da Shekaru Biyar Masu Zuwa Ko Menene Kudirinsa Na Rayuwa Da Yake So Ya Cimma.

3: Ki Tambayeshi Ko Yanada Wata Wacce Yake So Bayanke. Haka Nan Ko Ya Taba Aure.

4: Ki Tambayeshi Babban Burinsa A Rayuwa.

5: Ke Tambayeshi Akwai Na Kusa Dashi Da Sukayi Aure Suke Zaune Da Iyalansu.

6: Menene Burinsa A Wannan Soyayyar Da Yake Mike.
 
7: Hi Kokari Ya Fahintar Dake Yadda Ya Fassara Kalmar Soyayya Tun Bayan Haduwarku Ko Yana Samun Kula Irin Yadda Masoyi Ya Kamata Ya Samu Daga Wajen Masoyiyarsa. 

8: Tambayeshi A Mafimtarsa Me Ake Nufi Da Aure.

9: Tambayeshi Irin Rayuwar Da Yake Burin Yi Da Matarsa.

10: Tambayeshi Matsayinki A Wajen 'Yan Uwansa Da Abokansw Ko Sun San Da Zamanki.

11: Tambayi Ra'ayinsa Game Da Haihuwa.

12: Ya Fahintar Dashi Irin Akidarsa Na Addini.

13: Tambayeshi Lokacinda Yake Niyar Turowa Gidanku Da Kuma Ranar Da Zai Gabatar Dake Wajen Na Kusa Dashi Ko Iyayensa.

14: Tambayeshi Matsayin 'Yan Uwanki A Wajensa.

15: Nemi Ra'ayinsa Akan Yawan Matan Da Yake Burin Rayuwar Aure Dasu Nan Gaba.
 
Ba ana nufin ki saka manemin aurenki a gaba kina jera masa wadannan tambayiyin ba.

Ba kuma ana nufi daga randa yazo zaki addabeshi da tambaya ba. Sannu a hankali musamman bayan 'yan makwanni da soma soyayyar naku zaki rika jefa masa wadannan tambayiyin daya baya daya.

Kada ki manta duk wani tambayan da zaki masa cikin wadannan tambayiyin amsar da zai baki yana da matukar mahimmanci wajen yanke hukunci soyayya da shi ko kuma korarsa. Don haka ki maida hankali sosai a lokacin da yake baki amsar kowace tambaya.

Allah Ya bada sa'a. Allah Ya fidda mata masu kamun kai daga sharrin maza maciya amana da yaudara.

Post a Comment

0 Comments