Hanyoyi Guda 6 Da Zaku Iya Kaucewa Yawan Sha'awar Jima'i:


Hanyoyi Guda 6 Da Zaku Iya Kaucewa Yawan Sha'awar Jima'i:

SHARE 🔵
#Tsangayarmalamtonga 

Sha'awa wani halitta ne da yake tare da duk wani Dan Adam har ma da dabbobi musamman masu cike da lafiya a jikunansu.

Sau da dama sha'awa ya saka wasu mutane jin kunya a rayuwarsu, wasu kuwa har zaman kaso yake sasu saboda yadda suka kasa iya jimrewa sha'awar dake tare dasu.

Babu shakka a duk lokacin da sha'awar mutum ya motso, dole ne shi ma fa sai ya motsa koda kuwa motsin na neman yadda zai danne sha'awar ne.

Ga wasu hanyoyin da zaka iya amfani dasu domin kaucewa ingiza sha'awa.
 
1: Akwai wasu marasa aure da suke yawan amfani da magunguna da motsa sha'awa.

Irin wadannan magunguna suna tasiri a jikin mai yawan amfani dasu ta yadda zai jima yana aiki a jikinsu koda sun daina amfani dasu.

Kada ka sake ka rika amfani da irin wadannan magungunan musamman idan baka da auri ko baki da auri. Ko masu auren ma idan aka samu akasin da guda daga cikinsu ya samu uzurin rashin yin Jima'i, dole wannan daya Sha maganin zai cutu.

Don haka muddin mutum yana neman ya rage yawan sha'awar Jima'i a tare da shi, ya kaucewa Shan wadannan magungunan.

2: Duk wani mutum namiji ko mace sunsan irin nau'in halittar dake motsa musu sha'awa. Wasu mazan da zaran sunga manyan nonuwa ko duwawu shikenan babu zaman lafiya. Akwai matan da gashin jikin namiji kawai yake motsa su.

A bisa kuskure idan mutum yayi arba da irin wadannan halittun dake motsa masa sha'awa sai ya kauda kai kamar yadda shariya yace domin gudun fitina.

Ci gaba da kallon mace, ko namijin dake motsa muku sha'awa shi zai iya hana mutum sukunin da sai ya aikata ba dai-dai ga marasa aure kamin za a samu sa'ida.

 Amma idan kallo daya na kuskure aka yi aka kauda kai, za a samu sauki. Shi yasa addini ma bai tsananta akan irin wannan kallon ba saboda kusan dole ne musamman mutanen da suke cikin wadanda basu rufe tubarrajinsu.

3: Bayan gani da idanuwa akwai kuma tunanin abubuwan da zasu iya motsawa mutum sha'awa.

Yanada kyau duk mutumin dake da karfin sha'awa daya kaucewa yin wasu dogayen tunanin da zasu iya sa sha'awar sa ya motsa. Maimakon haka akwai tunanin da zasu fi maka amfani a rayuwa maimakon wannan da zai dagula maka lissafi babu wanjen biyan bukata na halas.

4: Baya ga gani da kuma tunanin abubuwan da zasu motsa mana sha'awa.

 Akwai kuma kallon abubuwan da zasu iya motsa mu.

Hotuna na batsa da finafinan batsa nan take zasu hargitsawa mai karfin sha'awa lissafi.

Duk wanda yake son kaucewa motsa sha'awar sa ba bisa ka'ida ba. Dole ne ya guji kallon hotuna ko finafinen da zasu tayar masa da wannan sha'awar nasa, ko nata.

5: Duk wani namiji ko mace sunsan abunda cikin sauki yake motsa musu sha'awa. Don haka a tabbatar an kiyaye su.
Kada a baiwa wadannan abubuwan daman shigo cikin rayuwar mutum a lokacinda ba a bukatar su.

Abunda yake motsawa wani sha'awa wani kuwa kwantar masa da shi yake yi. Don haka kada ka dauka zaka iya yin komai a gaban kowa da nufi bazai ji komai ba. Akwai maza da Matan da ko jinsu suka kalla suna jin sha'awa koda kuwa basu taba yin Luwadi ko Madugo ba.

6: Kadaici yana cikin abunda yake motsawa mutane sha'awar su da sauri.
Da zaran mutum ya samu kansa a cikin kadaici sai kuma ya soma tunanin da har zai jawo sha'awar sa ya motsa.

Domin kaucewa motsa sha'awar ka a lokacin Kadaici sai ka zasu damar karanta Alkurani mai tsarki ko kuma ka sa kanka yin wasu salloli na ibada da zasu dauke maka lokacin wannan kadaicin da zai iya jefaka cikin tunanin da sha'awa zai motso.

 
Wadannan wasu ne daga cikin hanyoyin da mutum zai iya kaucewa motsa sha'awar sa.

Sai dai akwai mutanen da suke da karfin sha'awa a halicce, da masana suke musu kallon kwakwaluwansu ya tabu.

Irin wadannan mutanen idan da zasu kwana su yini suna jima'i suna rabu da wanda ko wacce suke yi tare, zasu ji sabuwar sha'awa tamkar basu taba yin Jima'i ba a rayuwarsu.

Idan kana da irin wannan halitta ko haka halittar ki yake na sha'awa. Mu hadu a darasi na gaba.

Post a Comment

0 Comments