Amfani da koren ganyen shayi wajen kwalliya:

Amfani da koren ganyen shayi wajen kwalliya:

Amina Abdullahi

Ganyen shayi na da amfani a jikinmu domin shan sa na kara lafiya da kuma rage gautsin fata.

Kowane ganyen shayi na da nasa amfani a jiki, amma koren ya fi mahimmanci. Za a iya shafa ganyen shayin a fuska.


Koren ganyen shayi na kare fata daga saurin tsufa. Baya haka, yana kuma kare jikinmu daga cututtuka da dama.

Yawan shan koren ganyen shayi na sanya a ga mutum kamar saurayi ko ya yi shekaru.

Hanyoyi da za a iya amfani da koren ganyen shayi.

• Amfani da koren ganyen shayi:

na rage warin baki: A tafasa ganyen shayi. Bayan haka, sai a jira na tsawon minti 30. Sai a rika amfani da shi wajen wanke baki. Yin hakan na hana dauda zama a kan hakora. Kuma zai hana bakin wari.

• Shan shayin na rage kiba: za a iya
shan shayi safe da yamma domin rage maikon jiki.

• Koren shayi na rage tunbi ga macen da ta taba haihuwa da wadda ba ta taba haihuwa ba.

Shan ganyen shayi mara sukari akalla sau biyar a rana na matukar rage tunbi ga mata, musamman ma macen da ta taba haihuwa.

Gwara a gyara tunda ba a kwalliya da tunbi. Yana da kyau a jure na tsawon watanni biyar za a yi matukar mamaki da yadda tunbi zai baje.

• Ganyen shayi na magance ciwon
ido: A sanya ganyen shayi a firinji na
tsawon minti biyar, sannan ana daura
a kan idon har sai ya narke. Yana rage ciwon ido mai zafin nan.

Yana gyara fuska:

• A samu koren ganyen shayi sannan a zuba burbudin a cikin zuma sai a rika shafawa a fuska na tsawon minti 20, akalla sau biyu a rana, safe da yamma. Yin hakan na magance fesowar kurajen fuska.

• Za a iya amfani da koren ganyen
shayi a fuska; Akan sanya wannan ganyen a mayuka da dama na shafawa. Domin ganyen na kunshe da sinadarin Vitamin C da A da kuma E. Amfani da ganyen na rage maikon fuska kuma fuskar ta yi santsi yadda ko alamar kuraje ba za a ji ba.

Za a samo mayonnaise sai a dibi cokula uku. Sannan a zuba dakakken koren ganyen shayi. Za a rika shafawa a fuska ban da gefen idanu. Sai a bar shi na tsawon minti 20, sai a wanke da ruwan dumi.

Post a Comment

0 Comments