Yadda Za A Magance Fitowar Gemu A Fuskar Mace
Amina Abdullahi
Sallama a gare ku tare da fatar alheri. Gemu ga ’ya mace na daya daga cikin abubuwan da ke bata kwalliyarta. Domin yana bata mata adonta.
Sai a ga duk hoda da fandesho da aka sanya ba sa maganin haka.
Don haka ne a yau na kawo muku hanya mafi sauki da za a bi don magance fitowar gemu a fuskar mace.
Za a iya rabuwa da gemu a fuska idan an yi amfani da man cire gashi a jiki kamar (hair remobal cream). Sannan a samu auduga a jika da ruwa a goge wajen da aka cire gemun.
Kurkum na kara taimakawa bayan an cire gashin wajen sai a shafa kurkum domin kada ya nuna alamar cire gashi daga inda gemun ya fito.
Yana da kyau a kwaba kurkum da zuma sannan a shafa a fuska kafin a kwanta barci. Yin haka na kare fuskar daga sake fitowar wani gashi.
Amfani da nikakken karas da nono ko madara na kara gyara inda gashin ya fito.
A samu soda na girki a kwaba da ruwan lemun tsami sannan a rika dangwalawa da auduga ana shafawa a inda gashin yake fita na tsawon minti biyar a kullum kafin a wanke da ruwan dumi.
Sai a rika kulawa da irin man da ake shafawa a fuska domin idan man masu fitar da gashi ne a jiki wannan zai kara fesowar wasu gashin a fuska.
Domin rabuwa da irin wannan matsalar ta hanyar sauki. Shawarata ita ce kada a yi amfani da wani man kanti ko sabulu.
Sai a yi amfani da wadannan misalai da na bayar domin samun biyan bukata.
SHARE 🤶
0 Comments