Wasu Kurakuren Da 'Yan Mata Sukeyiwa Sabbin Samarinsu:


Wasu Kurakuren Da 'Yan Mata Sukeyiwa Sabbin Samarinsu:

SHARE 🤶
#tsangayarnalamtonga 

Yanada matukar wahala ka samu macen da bata aikata irin wadannan kurakuren a farkon soma soyayya da namiji.

Irin wadannan Halayen da matan ke nunawa yake koran wasu mazan dasuka zo nemansu da aure.

Mata, ga wani kwafsin da kuke yiwa mazan da suka zo nemanku sabbin shiga da sunan ku nan daga aji kuke.

 
Kin Fitowa Da Wuri:

A farkon zuwa wajen mace idan kayi sallama da ita idan a gida ka sameta sai tayi kusan awa guda bata fito ba kawai tana zaune tana bata lokaci daga maka aji.
Haka ne kina iya daga masa aji, amna barin mutum yana jiranki na tsawon awa guda wauta ne ba burgewa bane. Idan kina yi ki gyara kuskure ne.


Amsa Waya:

Wasu 'yan matan musamman wadanda zaka samesu a wajen aiki, makaranta ko wajen sayayya, muddin suka fahimci cewa kana son ka musu magana ne sai su tsawaita maganar da suke yi a waya su saka jira haka nan kawai.

Ki sani namiji na iya sauya raayinsa cikin dan karamin lokacinda kike amfani dashi na ja masa aji.

Mutunci ne ki katsai wayarki ki saurareshi daga nan ki ci gaba da wayar taki wannan shine abunda zai yiwa mai sonki tasiri a zuciyarsa bayan kun rabu.

Amma idan kina hakan ne da sunan daga aji tabbas zaki kori ladanki kina ji kina gani.

Yawan Surutu:

Akwai kuma matan da haduwarsu da namiji na farko kenan amma su kama zuba suna surutu da babu abun kamawa.
Maza suna daukan irin wannan macen ba mai kamun kai bace. Bisa al'ada na Dan Adam har sai yayi sabo da mutum yake sakin jikin da zai rika masa zuba.

Don haka ki kama kanki a farkon haduwarki da saurayi, ki natsu, ki bashi damar shi yayi maganar data kawo shi naki saurare da bada amsa a inda yazo da tambaya,amma ba surutu ba.
 
Neman Sanin Rayuwarsa:

Yana da kyau kisan rayuwar wanda yazo nemanki da aure amma ba daga farkon zuwansa ba ki soma tambayarsa a ina yake aiki, nawa ne albashinsa, ya taba soyayya, mai yasa ya rabu da wancan.

Duk tambayoyi ne da suka dace kiyi, amma ba a ranar da kuka soma haduwa ba. A ranar da kuka soma haduwa wannan ranar tashi ce ya gabatar da kansa ya kuma yi miki tambaya shikenan.

Gaba idan ya ci gaba da zuwa kuma kina da ra'ayinsa a nan ne zaka bijiro da tambayoyin da zakiyi kokarin saninsa.

Saurin neman sanin tarihin mutum na iya koran miki saurayi koda kuwa kinyi hakan ne da kyankyawan niya. 

Daukan Abu Maitsada;

Akwai matan da suke ganin su masu wayo ne ko son banza, da hakan kuma suke koran samarinsu ko mazan da suka zo aurensu ba tare da sun sani ba.

Akwai mazan da suke gwada mace a farkon haduwarku ta hanyar miki sayayya na ki zabo da kanki, ko kuma kai shagunan cin abinci ko kayan makulashe.

Abun haushi zakaga budurwa bata cin abincin ko bata saba da shi ba amma saboda son banza da karya zata ce shi take so. Pizza, shawarma, kaza. Kuma ke ko a gidanku ba ci kike ba kuma shi mai son naki yasan hakan.

Haka idan aka shiga dasu super Market suyi ta daukan abunda basuma taba ganinsa ba. Maza masu hankali daga wannan ranar bazaki sake ganinsa ba. Ba domin bai da kudin saye bane sai ya fahimci ke ba matar aure bace.

Ki zama mai saukin kai, duk juyin da zai yi kada ki dauki abunda ya wuce naira 200. Haka idan shagon abinci yakaiku kada ki dauki abunda ya wuce juice ko lemun kwalba, idan hakan ya zama dole kenan.

Kada kuma kice kowa ba tare dake sai an saya masa idan bake kadai bace.
 
Mata da dama sun kasa ganowa. Maza mayaudara sune suke jimre irin wannan wautar amma ba namijin daya zo aurenki da gaske ba. Domin shi rayuwa zaiyi dake na har abada. Shi kuwa mayaudari daga randa ya samu galaba akanki ko kulikuli kin daina ci ta hannunsa.

Don haka sai a kula, a kuma gyara.

Post a Comment

0 Comments