Kurakuran Mata Wajen Kaurace Wa Kwanciya Da Maigida Lokacin Al’ada


Assalamu Alaikum! Barkanmu da sake kasancewa tare da ku a cikin wannan shiri, wanda ke dauko matsalolin ma’aurata musamman bangarorin da suka shafi mata. A yau ma kamar kullum muna dauke da sabon Maudhu’i mai taken;

“Kaurace Wa Maigida Wajen Kwanciya Yayin Jinin Al’ada Ko Jinin Bik’i”.

Tabbas! Haramun ne namiji ya sadu da mace a irin wannan lokacin da take jinin Haila ko Biki, wanda akan samu wasu mazan da ba ruwansu da wannan ko da tana jinin sai ka ga ya kusanci macen, gashi a Alkur’ani Allah (S.W.A) yana cewa “Suna tambayar ka game da haila. Ka ce:

 “Lallai kazanta ce, saboda haka ka nisanci mata yayin da suke haila, kuma ka da ku kusance su sai sun yi tsarki… sannan idan sun yi wanka sai ku zo musu ta inda Allah ya umarce ku, hakika Allah yana son masu yawan tuba, kuma yana son tsarkaka”. (bakara Aya ta 222).

Wannan yana nuna haramcin saduwa da mace yayin Haila ko Biki, har sai idan ta yi tsarki. Amma sai dai hakan ba yana nufin ki dunga gudun mijinki bane ko ya zamana kin sake saboda kina jini ba wata kulawa da ya kamata, kasancewar wasu mazan musamman na wannan zamanin kan shiga wani yanayi ko damuwa a irin wannan lokacin. Zai iya kusantarki kamar yadda Nana Aisha (RA) ta ce idan tana Haila ta kan yi kunzugu ta kwanta da Manzon Allah (S.A.W).

Kusakuran Da Mata ke yi…

1. Wata matar don tana jinin Haila ko ta Haihu, sai ku gaba daya ta kaurace wa mijinta inda ko kwana daki daya ma sai ya gagara bare kuma a kai ga ado. Tabbas! ‘yar uwa wannan kuskure ne babba kike tafkawa, yana da kyau in kina wannan yanayin ki zama mai kulawa da tsabtar kanki tare da mijinki, akwai hanyoyi da za ki bi wajen gamsar da mijinki. Amma kamar ko yaushe da na saba tuna mana da tsabta ki tabbatar a tsaftace kike ki yi wanka ki sa auduga turare ya zamana kina kamshi saboda wasu matan in suna al’ada za ka samu jininsu mai karni ne sosai. To ko ma dai ya ne ki je masa a tsaftacwe.

2. Wata matar ba in tana al’ada bata san ta canza Auduga ba wata zata iya wuni ta kwana da Auduga guda daya a jikinta wanda hakan nada effects sosai ga lafiyarsu batare da sun sani ba. Wannan na daga cikin matsalolin Mata A Yau kwarai da gaske inkun duba zakuga infection yayi yawa sosai a wannan zamanin. Domin lafiyarki kikare kanki basai ciwo ya shafe kiba…kuma rashin sauya Auduga akan lokaci nasa Farjin mace karni wand aba al’ada take ba Miji na kusantarta yana jin k’arni is bery irritating dole kiga sauyi a kula.

3. Wata matar in ta gama jini ba za ta tsaya ta gyara jikinta yadda ya kamata ba akwai abubuwa da yakamata in kin gama ya zamana kin tsafatacce kanki musamman don guje wa karni da cututtuka akwai sabulai na Habba da Zaitun ga uwa uba Almisk ki yi kokari wajen tsarki da su a kula Mata in kin kula za ki ji dadin jikinki ki kuma tsare kanki da cututtuka, mijinki ba zai dunga shiga damuwa a ire-iren wadan nan lokutan.


A nan za mu dasa aya sai mun sake kasancewa da ku a shiri na gaba don jin mu dauke da sabon maudhu’in.

 

Post a Comment

0 Comments