Wasu Kurakuren Da Masoya Suke Yi Bayan Sun Rabu:


Wasu Kurakuren Da Masoya Suke Yi Bayan Sun Rabu:

#tsagayarmalamtonga 

Daya daga cikin dacin soyayya shine a lokacinda aka zo rabuwa.

Tabbas rabuwa na masoya babu dadi, amma idan hakan yazo babu makawa sai ya kasance.

Sai dai masoya da dama, wadanda suka yi aure dama wadanda basu yi sukan tafka wasu Kurakure bayan sun rabu da juna. Irin wadannan kurakuren sukan iya yiwa mai yinsu illa wani lokacin ma ya taba lafiyarsa.

Ga wasu kurakuren da masoya suke yi bayan sun rabu da juna.

 
1: Akwai masoyan da suke ganin har abada bazasu sake samun masoyi ko masoyiya irin wanda suka rabu dasu ba. Haka yasa sai suki baiwa wasu masu sonsu dama.

Ba karamin kuskure bane masoya su dauka cewa tunda sun rabu da wanda suka saba dasu bazasu sake samun kamarsu ba ko kuma duk irin halin masoya zai kasance daya ne, don haka bazasu kula kowa ba.

2: Wasu masoyan idan sun rabu da masoyansu sai su kauracewa mutane. Irin wadannan masoyan za a ga sun kadaita kansu ko kuma so saka talabinjin a gaba suna kallo. Basa fita kuma basa yin komai awannan lokacin.

Kuskure ne mutum ya takura kansa saboda ya rabu da masoyinsa. Shiga cikin mutane da ci gaba da mu'amala kamar yadda mutum ya saba shine zai yi saurin kawarwa mutum damuwar da yake cikin na rabuwa da masoyinsa.

3: Kada ku damu da kuskuren daya riga ya jawo rabuwarku koda wanene da laifin rabuwar. Sai dai wannan kuskuren ya zama darasi domin kaucewa gaba.

Yawan magana akan kuskuren zai rika sosa rai tari da cutar da zuciyar mai wannan tunanin. Don haka manta da abunda da ya riga ya wuce kawai tari gaba.

4: Kada ku nemi tilastawa masoyin dayayi sanadiyar rabuwarku dole sai ya ciga ba da wannan soyayyar. Neman yin hakan kuskure ne da zai sake sosawa mai bukatar hakan rai, ya kuma kara jawo tsana ga wannan daya nemi rabuwan. 

Fita batun soyayar, yi tamkar baku taba wata rayuwa tare ba.

5: Kada ku sake ku yiwa juna bakaken kalamai bayan rabuwarku. Wasu masoya da dama suka furta wasu maganganun da basu dace ba ga junansu saboda sun rabu.
Ana iya samun fahimta bayan rabuwarku da zaku ci gaba da soyaya ko zaman aurenku, amma wadannan maganganun da kuka futawa juna suna iya tsayuwa a zukatanku.
 
Wadannan kadan kenan daga cikin wasu kurakuren da masoya suke tafkawa bayan samun matsala ko rabuwa a soyayar su.
Da fatan za a kula kuma a gyara.

Post a Comment

0 Comments