Wasu Halayen Maza Da Mata Basu Fahimce Su Ba:


Wasu Halayen Maza Da Mata Basu Fahimce Su Ba:

SHARE 🔔
#tsagayarmalamtonga 
Kamar yadda maza basu san wasu halaye da dabi'un mata ba. Haka nan matan wasu basu fahimci halayen da dabi'u wasu mazan ba.

Ga wasu halayen maza da ba duk mace ta fahimcesu a zahirinsu ba.

 
1: Yabo: Su mata suna daukar cewa su kadaine ya kamata a yaba musu suna ganin maza basu damu da yabo ba.
Duk namiji yana son yaji yabo daga bakin masoyiyarsa. Yabo na halitta, kwalliya, kyauta duk wadannan maza na matukar son a musu. 

2: Godiya; Duk namiji yana son a masa godiya a duk lokacin da yayi wani abunda ya cancanci hakan.

Sai dai mata basu daukan yiwa namiji godiya tamkar wani abune da maza suke gudunsa.

3: Rashin Kudi: Ba duk mata bane suka yarda cewa maza suna rasa kudi ba. Akasarin mata suna dauka duk lokacin da namiji ya fita dole ne sai ya dawo da kudi.
Wannan yasa wasu matan basa yarda da uzurin babu da samarinsu suke musu ko mazansu na aure ba.

4: Rashin Tunani: Mata na yiwa maza kallon suna daukansu marasa tunani. Wannan mata da dama haka suke yiwa maza wannan tabon.

Sai dai a zahiri mazan da suka mallaki hankalin su basu iya aiwatar da wani abun har sai sunyi sha'awar da matansu ko iyayensu ko kannensu mata.

 
5: Maza Basuda Tunani Sai Na Jima'i: Yawancin mata suna dauka maza basu da abunda yake damunsu a rayuwa da ya wuce Jima'i. 

Wannan yasa da zaran ka yiwa mace magana ko taimako kawai abunda zai fara zuwa mata a rai kana sonta ne.

6: Duk Namiji Yana Zina: Mata da dama gani suke duk wani namiji sai yayi zina a rayuwarsa.

Akwai maza da damar gaske a duniya dabasu taba zina ba kuma basu da sha'awar yi. Wasu mazan sun gwammace gabansu ya mutu ko Allah Ya dauki ransu dasu yi zina.

7: Mikewar Gaba: Mata na dauka a duk lokacin da gaban namiji ya mike alamu ne na yana bukatar mace. Wannan ba haka abun yake ba.

Maza masu lafiya akalla gabansu yana mikewa a kullum haka nan kawai kaman sau 50 ko fiye a cewar masana.

Don haka ba wai da kin ga gaban namiji a mike ba ki dauka cewa Jima'i yake neman yi.

8: Ke Kadai Ce: Babban rashin fahimtar da mata suka yiwa maza shine na tunanin idan ya auri wacce yake so ba zai sake sha'awar wata macen ba.

Ba lalle bane dole sai namiji ya kara aure ba ko yayi zina ba. Sai dai duk wani namiji ko wani irin soyayya zaki yiwa mijinki, kuma komai kyauki sai namiji yaga wata yayi sha'awar ta koda bazai ce mata komai ba, sai yaji a ransa tayi masa. 

9: Kalmar So: Mata na daukan cewa duk namijin daya furta musu kalmar soyayya da gaske yake, sam ba haka bane.

Namiji zai iya furtawa mace kalmar yana sonta kuma bada gaske yake yi ba. Rashin fahimtar hakan yasa da zaran namiji ya cewa mace yana sonta sai ta sakar masa ranta da jikinta.

10: Jarumata: Akasarin mata suna daukan duk wani namiji jarumine bai da tsoro zai iya tinkaran duk wani abunda ya tinkaroshi.

Sai dai wannan fahimtar na mata ba haka yake ba a zahiri. Domin wasu matan ma sunfi wasu mazan jarumta. 

 
Wadannan wasu ne daga cikin tunanin da mata suke yi akan maza wanda kuma a gaskiyance ba haka abun yake ba.

Post a Comment

0 Comments